Sunday, 3 March 2019
Bamu yi nadamar kin zaben Buhari ba - Inji Inyamurai

Home Bamu yi nadamar kin zaben Buhari ba - Inji Inyamurai
Ku Tura A Social Media

Babbar kungiyar kabilar Inyamurai, Ohanaeze tace bata yi dana sanin kin zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasar daya gabata ba, tace idan za'a sake yin zabe sau dubu kuma shugaba Buhari ya tsaya takara to zata kara baiwa mabiyanta umarnin kada su zabe shi.

Kungiyar ta yi maganane ta hannun sakataren watsa labaranta, Uche Achi-Okpaga kamar yanda The Sun ta ruwaito, ya kara da cewa, shugaba Buhari be boye ba, ya bayyana karara cewa baya son kabilar inyamurai, ta hanyar nade-naden mukamai da maganganun shi da yake yi.

Yace Buharin ya bayyana cewa kaso 5 cikin dari kawai suka bashi a zaben 2015 dan haka baya yi dasu, yace duk da cewa a zaben 2019 ya samu kashi 25 cikin dari da ake bukata daga wasu jihohin Inyamuran duk da haka basa tsammanin zai canja irin kiyayyar da yake wa kabilar ta Inyamurai.

Yace, sun ji dadi yadda mutanen su suka yi musu biyayya akan zaben Atiku kuma suna so a canja fasalin kasar nan ta yadda kowace jiha zata dogara da kanta.

Yace idan aka canja fasalin kasa, Arewa ma sai tafi kudu samun ci gaba saboda yalwar kasar noma da yankin ke dashi amma sunki su gane. Yace a yankinsu an yi zabe me kyau ba kamar a wani yanki ba.

Saidai wata kungiyar ta Ohanaeze data balle daga uwar kungiyar, tuni ta taya shugaba Buhari murna sannan tace nan bada dadewa ba zata kai masa ziyarar taya murna da mubaya'a

Share this


Author: verified_user

0 Comments: