Labarai

Babban dalilin da yasa nake kira a zabi Ganduje – Inji Sheikh Kabiru Gombe

Babban Malamin addinin Musulunci, kuma sakataren kungiyar Jama’atil Izalatil Bidi’a wa Iqamatissunnah, Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana wani kwakkwaran dalilin da ya kamata jama’ar jahar Kano su sake zaban Gwamna Abdullahi Ganduje a karo na biyu.

Majiyarmu ta ruwaito Kabiru ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da yayi kuma aka nada, da a yanzu haka yake yawo a kafafen sadarwar zamani ana watsa shi, inda yace babban dalilin da zai fada ma Allah idan Ya tambayeshi akan me yace a zabi Ganduje shine Musuluntar da Maguzawa.

A jawabin nasa, Shehin Malamin ya bayyana yadda Gwamna Ganduje ya taba gayyatarsu zuwa Musuluntar da wasu maguzawa su dari biyu, da kiristoci guda biyu da suka nuna sha’awar shiga Musulunci.

“Allah Ya sani kuka na dinga yi a ranar da muka tafi musuluntar da maguzawan, saboda naga abinda ban taba gani ba, na san irin wahalar da muke sha idan muka shiga garin arna ko maguzawa kafin mu samu mutum 10 sun karbi musulunci, tare da bata tsawon lokaci. Amma sai gashi abin mamaki mutane 202 zasu musulunta a gabana, zasu karbi Kalmar shahada.” Inji shi.

Malam Kabiru ya kara da cewa shi da kasan mutane 20 ya baiwa shahada, shima shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau mutane 30 ya baiwa shahada, sai gwamnan jahar Kano daya baiwa kusan mutane 50 shahada, haka nan Shekarau ma ya bada shahada ga mutane 30.

Malamin yace haka sauran Maluma suka biyo baya suka yi ta baiwa maguzawanann Kalmar shahada, anayi ana canza musu suna, inda suke zaban sunan daya kwanta musu na Musulunci, har yace a gabansa wani mutumi ya bayyana musu cewa sunansa na yanka Jemage.

Daga karshe shehin Malamin ya tabbatar da cewa bayan kammala musuluntar da maguzawan, sai Ganduje ya raba musu kyautar kayan alheri, inda mata suka samu turmin zani da atamfa da jarin kudi, Maza kuma suka samu turmin shadda da jari.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button