Thursday, 21 March 2019
Atiku Abubakar Ya Biya Kudin Fansa Don A Sako Malam Ahmad Suleman kano?

Home Atiku Abubakar Ya Biya Kudin Fansa Don A Sako Malam Ahmad Suleman kano?
Ku Tura A Social Media


Daga : Datti assalafiy

Tun daren jiya labari ya iskeni kuma ana ta tambayata har da kiran waya cewa Maigirma Wazirin Adamawa Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Nigeria Alhaji Atiku Abubakar ya biya kudin da masu garkuwa da Malam Ahmad suka bukata don a sakoshi

Abinda ya faru shine; Akwai wata baiwar Allah Hajiya Maimuna Yusuf shugaban kungiyar Atiku Freinds Organization (AFO) sai a jiya Laraba ta samu labarin yin garkuwa da Malam Ahmad, sai tayi kokari wajen isar da kokenta kai tsaye zuwa ga Maigirma Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar don ya taimaka a kubutar da Malam

Maigirma Wazirin Adamawa ya bada umarni a biya kudin fansa da su masu garkuwa da Malam Ahmad suka bukata kafin su sakoshi, to amma sai aka samu wasu 'yan majalisar Wazirin Adamawa sukace su basu goyi bayan Atiku Abubakar ya biya kudin ba

Sunce saboda wai kungiyar Izala itace kan gaba wajen yakar Atiku Abubakar, bata bashi goyon baya ya zama shugaban Kasa ba, don haka tunda yanzu wani abu ya samu 'dan kungiyarsu sai suje Buharin da suka zaba ya musu, amma dai shi Atiku Abubakar yace ba komai zai iya biya, har zuwa hanzu ana kan tababa tsakanin 'yan majalisar Wazirin Adamawa

To wannan shine halin da ake ciki jama'a, amma tabbas Alhaji Atiku Abubakar yace zai biya kudin fansa don a saki Malam Ahmad, wannan shine abinda ya tabbata gaskiya ba kamar yadda kuka karanta a wasu gurare cewa Atiku ya biya kudin fansan, wannan shine amsar mutanen da suke ta tambayata game da wannan batun, da kuma wadanda suke jira su ga nayi magana a kai

Muna rokon Allah (SWT) Ya kawo wa Malam dauki ta inda ba muyi zato ba
Yaa Allah Ka sakawa Alhaji Atiku Abubakar sakamako da gidan Aljannah Madaukakiya Amin

Share this


Author: verified_user

0 Comments: