Tuesday, 5 March 2019
Al'ummar Jihar Bauchi sun Yi Tir Da Allah Wadai Da Kalaman Nura Hussain

Home Al'ummar Jihar Bauchi sun Yi Tir Da Allah Wadai Da Kalaman Nura Hussain
Ku Tura A Social Media

Daga Salama Muhammad Rigasa

Tun bayan da wani dan wasan Hausa me suna Nura Hussaini ya saki wani Hoton Bidiyo da ke furta kalaman batanci ga Gwamnan Jihar Bauchi, M.A, al'ummar Jihar Bauchi su ke tir da Allah wadai da shi.

Domin kamar yadda jama'a su ka sani, wannan mutum Nura Hussaini, ba mutumin arziki ba ne, kuma ba shi da wata kima da daraja a idon al'umma.

Har takara ya taba tsayawa a mazabarsa amma saboda mummunar dabi'a tasa al'umma su ka yi masa korar kare ya koma wasan Hausa, ya ke shiga rigar malanta ya ke fitowa a ustazu, ya na ci da addini.

Yanzu kuma harkar fim din Hausan ma ta ki shi ba a damawa da shi, shi ya sa ya koma cin mutuncin manyan mutane kamar yadda ya yi wa Shaik Gumi a kwanakin baya, yanzu kuma ya dawo kan gwamna M.A domin ya bata masa suna a idon al'umma.

To dan haka, ga wanda bai san waye Nura Hussaini ba, ya sani, kasurgumin fasiki ne, kuma yanzu haka ba shi da wata babbar sana'a da ta wuci (kawalci) ya na diban 'yan mata ya na kaiwa manyan mutane su yi lalata da su su biya shi.

Kuma da ya ke maganar wai shi dan Siyasar Buhari ne, ai duk Duniya ta gani, ranar da Buhari ya zo Bauchi kaddamar da yakin neman zabe, ya daga hannun gwamna M.A ya ce wa al'ummar Jihar Bauchi "APC SAK".

Kenan shi kansa shugaba Buhari ya yarda da nagarta da cancantar gwamna M.A, dan haka babu dalilin da Zai sanya su dauki hudubar wani fasiki dan tasha wai shi Nura Hussaini.

Al'ummar Jihar Bauchi su na nan tare da me girma gwamna M.A. Za kuma su fito ranar tara ga wata su sake kada masa kuri'unsu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: