Monday, 4 March 2019
Abinda Muke Fata Shugaba Buhari Ya Tabbatar Dasu A Arewa

Home Abinda Muke Fata Shugaba Buhari Ya Tabbatar Dasu A Arewa
Ku Tura A Social Media


Daga :Datti assalafiy

1- Shugaba Buhari ya duba girman Allah ya binciki hakikanin gaskiyar yanayi tsaro a jihar Zamfara ya kai musu daukin gaggawa

2- Shugaba Buhari yayi iya bakin kokarinsa ya tabbatar da an shafe ruhin kungiyar Boko Haram daga doron duniya kafin wa'adin mulkinsa ya kare

3- Shugaba Buhari yayi kokari ya tabbata an tona sauran rijiyoyin man fetur daga arewa, irin wanda akeyi a yankin kogin Kolmani dake karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi, an kuma fara sayar da danyen man fetur na arewan a kasuwannin duniya kafin wa'adin mulkinsa ya kare

4- Shugaba Buhari ya tabbata tashar samar da wutar lantarki da ake ginawa a tsibirin Mambila yankin Karamar hukumar Sardauna jihar Taraba mai karfin megawatts 3050 ya fara aiki kafin wa'adin mulkinsa ya kare

5- Shugaba Buhari ya tabbata cewa manyan jiragen ruwa sun fara sauke kayan da suka dauko daga Kasashen duniya a sabon tashar jirgin ruwa na arewa (Baro Port) da aka gina a karon farko cikin tarihin Nigeria kafin wa'adin mulkinsa ya kare

6- Shugaba Buhari yayi kokari ya dage ya tabbatar da cewa jiragen Kasa sun fara zirga a Arewa zuwa Kudancin Kasar, wato tun daga jihar Maiduguri zuwa Lagos kafin wa'adinsa ya kare

Idan shugaba Buhari ya tabbatar da wadannan abubuwa guda shida a arewa to da ikon Allah arewa zata tsayu da kafafunta, tabbatar da wadannan ayyuka a arewa zasuyi sanadin magance zaman banza, sace sace, barace barace, za'a samu raguwar aikata miyagun laifuka da sauransu

Idan wadannan ayyuka suka tabbata, za'a gina sabuwar arewa, 'yan arewa zasuji dadin rayuwa, kayan abinci da na masarufi zaiyi sauki, mutane daga sassan duniya zasuyi sha'awar zuwa arewa, manyan kamfanonin duniya zasu shigo arewa, tattalin arzikin arewa zai bunkasa, arewa zata kara samun yawan al'umma kimiyya da fasaha ya karu

Duk wanda yake da kishin arewa ya dage da taya shugaba Buhari da addu'ah Allah Ya bashi ikon tabbatar da wadannan manyan ayyuka a arewa, idan shugaba Buhari ya tabbatar dasu to duk abinda zai faru a Kasar bayan gushewar Buhari to ita dai arewa tana tsaye da kafafunta

Muna rokon Allah Ya bawa shugaba Buhari ikon tabbatar da wadannan manyan ayyuka a arewa kafin wa'adin mulkinda ya kare Amin

Share this


Author: verified_user

0 Comments: