Saturday, 30 March 2019
Abin da ya sa ban yi wa kowane dan takara kamfe ba – Nafisa Abdullahi

Home Abin da ya sa ban yi wa kowane dan takara kamfe ba – Nafisa Abdullahi
Ku Tura A Social Media
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi wadda aka fi sani da ‘Nafisa Sai Wata Rana’ a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, ta ce ta ki yi wa kowane dan takara kamfe ne saboda ba ta so ta tilasta wa masoyanta su zabi ra’ayinta.
Nafisa ta bayyana haka ne a wata hira da shafin sadarwa na Kannywoodscene a makon jiya.

A lokacin da aka tambayi jaruma Nafisa wadda ta fara fitowa a fim tana ’yar shekara 19 a cikin wani fim mai suna ‘Sai Wata Rana’ a shekarar 2010 kan dalilin da ya sa ba ta shiga tafiyar ’yan fim da suke yi wa ’yan siyasa kamfe ba, sai ta ce, “Ba na so in tilasta wa masoyana su zabi dan takarar da nake yi wa kamfe, na fi so su zabi ’yan takarar da su suke so.”
Da aka tambaye ta ko me ya sa ba ta nuna goyon baya ga Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ko wanda ya yi wa Jam’iyyar PDP takara, wato Abba Kabir Yusuf ba, sai ta ce, “Wannan ba hurumina ba ne, kowa yana da ’yancinsa.”

Jaruma Nafisa wadda ta zama Gwarzuwar Jaruma a lokacin Gasar Kannywood Awards a shekarar 2014 ta ce a yanzu tana shigar Turawa ne saboda tana da ra’ayin hakan, “Kamar yadda a da nake sa atamfa da doguwar riga, yanzu ma na yi ra’ayin sa kayan Turawa ne.”
Da aka tambayi jarumar wadda take shugabancin kamfanin shirya fim na Nafs Entertainment ko me take yi don ganin tauraruwarta ba ta dusashe ba, sai ta ce, “Kun sani ba tun yanzu ba, ba na fadi tashi don ganin tauraruwata ba ta dusashe ba, ina yin abubuwa ne yadda nake so a lokacin da nake so, ba tare da tunanin maganganun mutane ba.”

Share this


Author: verified_user

0 Comments: