Wednesday, 27 February 2019
Zaben 2019: INEC ta tabbatar da nasarar Buhari kan Atiku

Home Zaben 2019: INEC ta tabbatar da nasarar Buhari kan Atiku
Ku Tura A Social Media
An bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, abin da zai ba shi damar sake mulkar kasar na karin shekaru hudu masu zuwa.
Shugaban mai shekara 76, na jam'iyyar APC, ya kayar da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, da tazarar kuri'u kusan miliyan hudu.
Sai dai jam'iyyar adawa ta PDP, wacce Atiku ya yi wa takara, ta yi watsi da sakamakon zaben da Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Mahmood Yakubu ya bayyana da misalin karfe 4.30 na asuba.
Nan gaba kadan ne ake sa ran shugaban zai yi jawabin murna ga magoya bayansa, duk da cewa kawo yanzu abokin takararsa bai mika wuya ba.
Tun a sakamakon farko-farko da aka fara bayyanawa jam'iyyar ta yi zargin cewa akwai kura-kurai a zaben.
An samu jinkiri da kuma tashin hankali gabanin da kuma lokacin zaben sai dai masu sa'ido masu zaman kansu ba su ce an yi magudi ba.
Shugaba Buhari ya yi nasara a jihohi 19 daga cikin 36 na kasar, yayin da babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar ya samu jihohi 17 da kuma babban birnin kasar Abuja.
Buhari ya samu kuri'u 15,191,847, yayin da Atiku ya samu 11,262,978, kamar yadda Hukumar Zabe ta INEC ta bayyana.


sakamako

Tuni jiga-jigan jam'iyyar ta APC suka fara isa birnin Abuja domin taya shugaban murna, ciki har da babban jagoranta Sanata Bola Ahmed Tinubu.
Tun gabanin bayyana sakamakon zaben, mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar na PDP ya ce kuri'un da ake kirgawa "ba daidai ba ne, kuma ba za a amince da su ba."
Ya shaida wa BBC cewa, an yi aringizon kuri'u a jihohi da dama, inda ya bayar da misali da Yobe, da Borno da Sokoto da Nasarawa da Platue.
Tarayyar Turai da Amurka da Kungiyar Tarayyar Afirka sun nuna damuwarsu kan bata lokacin da aka samu wajen kai kayan zabe a ranar Asabar, amma babu wata kungiya mai zaman kanta da ta sa ido kan zaben da ta yi zargin cewa an yi zamba.
Wannan shi ne zabe da aka samu karancin fitowar jama'a a cikin shekara 20. Kasa da kashi 35 cikin dari na masu kada kuri'a ne suka fita domin yin zaben.
Buhari dan jam'iyya mai mulki ta APC ya fafata ne da Atiku Abubakar na PDP.
Kowace jam'iyya ta ce hukumar zabe ta INEC na aiki da dayar don sauya sakamakon zaben, wanda tun farko aka shirya yin sa ranar 16 ga watan Fabrairu, amma sa'o'i kadan gabanin a bude rumfunan zabe sai aka daga.


Shugaban PDP Uche Secondus ya ce gwamnati ta yi magudi a zaben.Hakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionUche Secondus ya koka kan sakamakon zaben tun kafin a kammala

Buhari ya yi alkawarin ci gaba da ayyukan da ya fara a karonsa na farko, yayin da Atiku, wanda babban dan kasuwa ne, ya soki Buharin da bata shekaru hudunsa na farko ba tare da yin abin a zo a gani ba.
Masu sharhi na ganin akwai manyan kalubale a gaban Buhari a yayin da zai fara karo na biyu, da suka hada da rashin isasshiyar wutar lantarki da cin hanci da barazanar tsaro da matsin tattalin arziki.

Mene ne zarge-zargen?

Tun kafin akai ga sanar da sakamkon karshe na zaben, Mr Secondus ya yi kakkausar suka kan "yadda gwamnati ta yi ta kokarin sauya al'amura,' a cewarsa.


Two men listen to the radio as Nigerians await the results of the Presidential election, in Kano, Nigeria February 24, 2019.Hakkin mallakar hotoREUTERS
Image caption'Yan Najeriya sun kasance cikin zakuwar son jin wa ya lashe zaben

A hannu guda kuma, gwamnatin tarayya ta soki PDP da "lalata zaben" da kuma jawo rikicin siyasa.
Zaben ya hada da na 'yan majalisar dattijai da wakilan tarayya.
A lokutan jefa kuri'a an samu zaman lafiya a a fadin kasar, sai dai mayakan Boko Haram sun kai wasu hare-hare a arewa maso gabas, sannan wasu 'yan daba sun yi kokarin satar akwatunan zabe musamman a jihohin Rivers da Lagos da kuma Anambra.
Wata gamayyar kungiyoyin fararen hula sun ruwaito cewa wajen mutum 16 aka kashe a fadin kasar a lokacin zabukan, yawan da bai kai na wadanda aka kashe a 2015 ba.
An kama wasu mutum biyu a Lagos bayan da wasu gungun matasa suka kai wa masu kada kuri'a hari, kamar yadda wani ganau Ralph Onodike ya shaida wa BBC.
Ya ce: "Abun da suka dinga fada shi ne, in dai ba jam'iyyar APC za ku kadawa kuri'a ba to za mu kai muku hari."

Yadda sakamakon yake a kowacce jihataswirar sakamakon zaben shugaban kasa na 2019

Yaya zaben yake aiki?

Dan takarar da ya fi samun kuri'u ake ayyanawa a matsayin wanda ya yi nasara a zagayen farko, in dai har ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri'un da aka kada a kashi biyu cikin uku na jihohin kasar.
'Yan takarar shugaban kasa 73 ne suka yi rijista, amma an fi yin gwagwagwar ne tsakanin Buhari da Atiku.
Dukkansu sun fito ne daga arewacin kasar inda musulmai suka fi yawa, kuma dukkansu sun haura shekara 70, yayin da mafi yawan 'yan kasar da suka yi rijistar zabe 'yan kasa da shekara 35 ne.

Tsari

Tsarin zabar 'yan takarar shugaban kasa an yi shi ne akan wadannan:
 • Jam'iyyu a majalisa
 • Sanannun jam'iyyu (masu dan takara wanda ba sananne ba)
 • Sanannun 'yan takara a jam'iyyu wadanda ba sanannu ba
 • Sananne a duniya yada labarai
 • Sananne a duniyar shafukan sada zumunta

Mai hoton

Getty, www.fela2019.com, atiku.org, tobuildanation.com, facebook, sowore2019.org

Wadanda suka hada wannan aiki

Shiryawa: Olawale Malomo. Bincike: Nkechi Ogbonna

Wadanne ne manyan batutuwan?

Najeriya ce kasar da ta fi kowacce arzikin man fetur a Afirka, amma cin hanci da gazawa wajen zuba jarin abun da ake samu daga arzikin ya jawo matukar ci baya.
Kusan kashi daya bisa hudu na matasan kasar ba su da aikin yi.


Presentational grey line

Zaben cikin alkalumma

 • Masu katin zabe mutum miliyan 82, 344,107
 • Kashi 51 cikin 100 na masu kada kuri'a 'yan kasa da shekara 35
 • Wadanda aka tantance 29,364,209
 • Kuri'un da ka kada 28,614,190
 • Kuri'un da aka yi watsi da su 1,289,607
 • 'Yan takarar shugaban kasa 73
 • Rumfunan zabe 120,000

Rahoto :bbchausa.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: