Monday, 18 February 2019
Yadda Ake Hada Kunun Alkama (Wannan Kunu Yana Kara Ni’ima)

Home Yadda Ake Hada Kunun Alkama (Wannan Kunu Yana Kara Ni’ima)
Ku Tura A Social Media
Abubuwa da ake bukata wajen hadawa;
– Alkama
– Aya
Yadda Ake hadawa:
Ki gyara Alkama wato ki wanke ki rege ki surfa saiki shanya, ita manaya ki surfa ki gyara ki shanya idan suka bushe sai ki hada guri daya ki kai a niko mi ki ki tankade sai ki debi garin ki dama da ruwan sanyin, sannan ki kwara tafashshen ruwan kamar dai yadda zaki dama kunun tsamiya, idan kika dama zaiyi kauri. Zaki iya sa lemin tsami idan kinaso saiki zuba sugar da madara in kinaso.
Zaki iya yima oga wannan kunu yayin buda baki ko karin kumallo. Wannan kunu yana kara ni ima.
Yadda ake kunun alkama:
Yau za muyi kunun alkama. Ga shi kamar haka:
Abubuwan hadawa
1. Alkama
2. Gyada Markadadde
3. Kayan kamshi
4. Suga
5. Nono

Yadda ake hadawa
1. Da farko za ki kawo garin alkama da wanda ba’a nika ba sai ki wanke alkamarki ki sa a tukunya ki dora a wuta.
2. Sai ki dauko gyadarki ki dama ki tace ki ajiye a gefe, sai ki duba idan ya yi sai ki sauke ki juye. Sannan ki dora ruwan gyada a wuta.
3. Idan ya tafasa sai ki dauko dafeffen alkamarki ki zuba ki barshi ya kara nuna.
4. Sai ki dama garin alkamarki kadan ki sa kayan kamshi.
5. Idan ya yi sai ki sauke ki zuba damammen garinki ki juya sosai.
6. Idan ya yi sai ki zuba suga da nono ki juya sosai ki sawa mai gida da yara.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: