Tuesday, 19 February 2019
TSARKI YA TABBATA GA ALLAH : Ash -Sheikh Abubakar Giro Argungu Ya Janye Kalaman Na Tsinuwa

Home TSARKI YA TABBATA GA ALLAH : Ash -Sheikh Abubakar Giro Argungu Ya Janye Kalaman Na Tsinuwa
Ku Tura A Social Media

Yanzunnan na kammala ganin sabon video da Ash-sheikh Abubakar Giro Argungu ya fitar yana mai janye kalmar tsinuwa da yayi ga wadanda basa son Buhari

Malam yayi cikakken bayani, yace videon da aka gani yana yin tsinuwa ga wadanda basa son Buhari tsoho ne tun a lokacin gwamnatin Jonathan, kuma yayi videon ba a cikin Kasarmu Nigeria ba, wasu ne suka fito da videon a yanzu don su cimma wata manufa tasu

Sheikh Abubakar Giro Argungu yace nayi wannan addu'ar ne ta tsinuwa lokacin da Kasarmu Nigeria take fama da matsalar ta'addancin Boko Haram a lokacin gwamnatin Jonathan, kuma a yanzu na gane cewa kuskure ne tsinuwar da nayi wa wadanda basa son Buhari


Wallahi na jinjinawa Malam Abubakar Giro Argungu, na kara jin kaunarsa ta ratsa ni, tabbas Malam Ahlussunnah ne na gaske, nima Datti Assalafiy ina mai neman afuwa bisa wasu kalmomi da na furta masu nauyi akan Malam, Allah Ya yafe mana gaba daya

Muna rokon Allah Ya albarkaci rayuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu, Allah Ka bamu ikon koyi da kyawawan halaye na Malam Amin

Share this


Author: verified_user

0 Comments: