Wednesday, 13 February 2019
TONAN ASIRI: Karanta wannan sakon yana da matukar mahimmanci

Home TONAN ASIRI: Karanta wannan sakon yana da matukar mahimmanci
Ku Tura A Social Media

Sharudan da Obasanjo ya gindayawa Atiku kafin ya mara masa baya a zabe mai zuwa.

Daga Barrister Abegunde O. Adebiyi.

A wannan lokacin siyasa ta dauki wani sabon salo na mamaki musamman lokacin da Obasanjo ya amince zai goyi bayan abokin gabarsa wato wazirin Adamawa.

Ina cikin Abekuta jihar Ogun lokacin da Atiku, Saraki, shugaban PDP da kuma wasu mutane wanda ban san su ba suka kawowa Obasanjo ziyarar sirri a gidansa dake Otta cikin dare.

Duk wanda ya asan gabar dake tsakanin Atiku da mai gidansa Obasanjo na san zai yi mamakin ganin Atiku a gidan Obasanjo cikin  dare haka.
Sai dai ni banyi mamaki ba saboda nasan irin haka tasha faruwa a siyasa, kaga abokan gaba sun hada kai domin su cimma burikansu na san zuciya.
Ganawar da sukai ta sirri ta kai ta tsowon awa biyu.

Muna zaune sai ga TY Danjuma da Aliyu Gusau da wasu sauran manyan yan kasuwar Man fetur sun shigo gidan suma.

Ganin wannan manyan mutane haka yasa na tambayi kaina anya wannan taron siyasane kadai kuwa? Ina ga bayan siyasa akwai kuma batun kasuwanci saboda naga manyan yan kasuwa agun.

Kafin su fara tattaunawa sai da aka kori kowa amma ni na yi sa'a ba ace na fita ba saboda albarkacin darajar mahaifina wanda ya turo ni nazo na wakilce shi a ganawar da zasuyi .

Sun fara tattaunawa misalin karfe 11 na dare sannan sun gama karfe 2:48 na safe. Gaskiya na dimauta matuka da jin abinda suke cewa, na san Obasanjo mugu ne amma  bantaba tunanin zaluncin nasa ya kai haka ba sai da nagani kuma naji da kunnena abinda suke kullawa.

 A nan sai na gane dalilin da yasa mahaifina da aka gayyace shi bai zoba sai ya turoni na wakilce shi.

Bana kaunar Buhari, amma ina yawan Tambayar kaine dalilin da yasa Obasanjo ya tsani Buhari da mutanen Arewa haka, na yi takaici da har yanzu ban san dalilin ba.

Babu bukatar sai na fadi duk abinda suka tattauna, abinda yafi mahimmanci shine na fadi sharudan da Obasanjo ya gindayawa Atiku kafin ya yarda ya mara masa baya don ya ci zabe.

1. Atiku ya sanya hannu akan lallai idan ya zama shugaban kasa zai bawa TY Danjuma rijiyoyin mai shida sauran yan kasuwar da suke a nan.

2. Ya sanya hannu akan bukatar Obasanjo ta idan Atiku ya zama shugaban kasa zai tsaida akin wutar lantarki ta MAMBILA.

3. Sannan zai tsaida aikin yashe tekun da ake yi daga Lagos zuwa Niger da kogi.

4. Zai hana yawon kiyon shanu da makiyaya suke yi a fadin Nigeria.

5. Sannan Idan Atiku ya shiga office zai tabbatar da ya dakatar da fasa bututun Mai da yan tawayen Niger Delta suke yi.

6. Sannan Zai dawo da tallafin man fetur wanda gwamnatin Buhari ta daina badawa.

7. Bayan haka, duk wata shari'a ta cin hanci da rashawa za'a dakatar da ita.

8. Sannan Atiku ya sanya hannu akan idan ya gama wa'adinsa zai mika mulki ga mataimakin sa PETER OBI.

Tunda naga Atiku ya sanya hannu akan sharudan da Obasanjo ya gindaya masa sai hankalina ya tashi na kasa samun natsuwa, wani lokacin idan na tuna ko bacci bana iya yi har sai da takai na fadawa Babana abinda ya faru a gun da ya tura ni na wakilce shi.
Mahaifina ya tabbatar min da matukar Obasanjo bai mutu ba to zai yi wuya Nigeria ta samu cigaba domin sai ya yi kokarin kawar da duk wani shugaba wanda ya ke da niyar kawowa kasa cigaba.

Abinda yafi damuna shine da naga Atiku ya amince da duk wadannan sharuda wanda babu alkairi cikin su, ashe burin Atiku na tsayawa takara har yafi cigaban al'ummah amfani?

Kamar yadda na fada a baya cewa ba zan iya fadin duk abinda suka tattauna wanda naji da kunnena ba amma iya wannan da na fada nasan  na sanya kaina cikin damuwa.
Na zabi na fadi ko da za'a kashe ni matukar dai na sanar da yan Nigeria abinda ake kokarin cutar da su dashi.

Fassara daga :
El Yunus El Shuaib.
Labari daga:
Barr. Abegunde O. Adebiyi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: