Sunday, 17 February 2019
Tambayoyi 20 ga Ahlusunnah masu raayin siyasa - Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Home Tambayoyi 20 ga Ahlusunnah masu raayin siyasa - Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Ku Tura A Social Media


1 Mai yasa muke da  shaawar laanta da tsinuwa da zagi da zargi, da mummunan zato akan addua da fatan alkhairi da kyakyawan zato.? akan raayin siyasa?

2 Mai yasa duk lokacin siyasa idan yazo muke shaawar Malaman mu subi raayin mu. Ko mu zage su?
3  Shin  acikin dukkan jamiyyu babu musulmi da kafurai?
4 Zabin Dan takara nassi ne ko ijtihadi?

5 Idan muka taru a guri daya muka zabi wata jamiyya kawai,  idan Allah ya jarabcemu wasu suka ci yaya za muyi?
6 Akwai wani Dan siyasa da yafi malami daraja?
7 Ni a wajena dukkan malaman da suke tare da Buhari da Atiku sunfi bukari da Atiku daraja a wajena don haka ba zanci mutuncin  wani malami ba akan raayinsa na siyasa. Kai fa?
8 Da bayyana sunan Dan takara da kuma bayyana siffofi a zabi mutum na gari mai amana wanne yafi dacewa?
9 Don Allah waye bashi da raayin siyasa ko wani Dan takara? Mai yasa raayinka shine maaunin gane malami na Allah, mara kwadayi?
10 Yaya ake tabbatar da mutum yayi laifi a sharia?
11 Mai yasa muke saurin yarda da dukkan abinda muka ji ko muka gani ko muka karanta, ba tare da binkice ba?
12 Mai yasa muke saurin yanke  hukuncin ridda da kafurci ga wani mutum na musamman  domin ya fadi wata magana ko yayi wani aiki ba tare da bin kaida ba ta ahlusunnah wajan takfir?
13 Idan wanda baya raayin wani Dan takara ko wata jamiyya yayi laifi,  kafirin cikin jamiyya yayi daidai ?

14 Wacce jamiyya ce babu nagari da fasikai?
15 Wacce Jamiyya ce babu Ahlussunnah ?
16 Ina hakkin musumi akan Dan uwansa musulmi?

17 Mainene laifin wanda yace ba zaiyi sak ba,  a sama zaiyi buhari a kasa cancanta?
18 Mainene laifin wanda yace ayi Apc sak  da wanda yace ayi pdp sak,  wa yake da nassin kurani ko Hadis?

19 Wa zaka bi a lahira ka tsira?
20 Waye zai tabbatar da shariar musulunci?
21 Mai yasa yan shia da Yan darika bakajin suna yiwa malaman su fitsara akan raayin siyasa?
Ko wacce tambaya maki uku, amma ka kawo hujja mai karfi.
ALLAH YA ZABA  MANA  NA GARI.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: