Friday, 1 February 2019
Siyasar Nigeria :Ya Kamata Mu Nemi Afuwar Sheikh Dr Ahmad Gummi - Datti assalafiy

Home Siyasar Nigeria :Ya Kamata Mu Nemi Afuwar Sheikh Dr Ahmad Gummi - Datti assalafiy
Ku Tura A Social Media


A baya can, mun kasance masu kausasa harce idan Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi magana akan siyasar Nigeria, a yanzu mun fahimci cewa munyi kuskure idan muna masa raddi akan abar banza siyasar Nigeria

Maganar gaskiya yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria lamari ne mai girma da rikitarwa wanda da wahala ace an kawo karshen cin hanci da rashawa, duk ta'asar da 'dan siyasa zai tabka, da duk irin cin amanar da zai aikata da satar dukiyar al'umma ko da tallafawa ayyukan ta'addanci ne, to yana dawowa cikin jam'iyyah mai mulki magana ya kare

Na taba jin Dr. Ahmad Gumi ya furta wata kalma wanda sai a yanzu ne na fahimci gaskiyar abinda ya furta, yace a batun yaki da cin hanci da rashawa karyane they are all corrupt
Duk inda mutum ya kai ga biyewa bangare daya a 'yan siyasar Nigeria to zai iya kunyata daga karshen al'amari

Allah Ya sauwake

Share this


Author: verified_user

0 Comments: