Friday, 1 February 2019
SHUGABA BUHARI ZAI KAFA TARIHI Za A Yi Bikin Kaddamar Da Rijiyoyin Man Fetur Da Aka Samu A Jihar Bauchi

Home SHUGABA BUHARI ZAI KAFA TARIHI Za A Yi Bikin Kaddamar Da Rijiyoyin Man Fetur Da Aka Samu A Jihar Bauchi
Ku Tura A Social Media


Daga Datti Assalafiy

Hukumar kula da albarkatun man fetur na 'kasa (NNPC) ta fitar da sanarwan cewa gobe Asabar 2-2-2019 shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabbin rijiyoyin men fetur da aka samu nasaran tonawa a yankin kogin Kolmani dake karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi.

Wannan shine karon farko a tarihin duniya da aka yi nasarar tona rijiyoyin man fetur a arewa kuma a karkashin gwamnatin shugaban 'kasa Muhammadu Buhari, sannan jihar Bauchi za ta shiga jerin jihohi masu arzikin man fetur a Nijeriya.

Wannan nasara ce daga Allah, Baba Buhari mun gode, Allah Ka taimaki shugaba Buhari Ka kara masa taimako da nasara. Amin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: