Friday, 15 February 2019
Sheikh Daurawa ya jagoranci Limamai sama da 100 wajen kaiwa Kwankwaso ziyarar goyon baya

Home Sheikh Daurawa ya jagoranci Limamai sama da 100 wajen kaiwa Kwankwaso ziyarar goyon baya
Ku Tura A Social Media


A yayin da malamai musamman na izala suka yi caa akan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso sakamakon kalamansa da ya yi akan wasu malamai da ya kira da ‘yan ci da addini ta hanyar kutsa kawunansu cikin harkar siyasa don su azurta kawunansu, shi kuwa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda shi ne kwamanda Hisaba ta jihar Kano, a daren jiya Alhamis ya jagoranci limamai sama da guda 100 sun yi kafa da kafa da har gidan Kwankwason don su nuna goyon bayansu a bayyane.
An dai jiwo Kwankwaso ne a wata hira da ya gabatar yana kalubalantar wasu Malamai da ya bayyana ‘yan ta moren siyasa da ke ajiye gemu da dage wando alhali kuma suna aikata wasu abubuwa da basu dace ba.
Wannan batu nasa bai yi wa Malaman Izala dadi ba cikinsu kuwa har da Sheikh Abdullahi Pakistan da Sheikh Giro Argungun da ma wasu da dama, inda suka zargi Kwankwaso da aibata sunar Annabi SAW.
Sai dai kuma a wani abu da ya yi kama da gaskata maganar Kwankwaso, Sheikh Daurawa ya jagoranci limamai sama da dari zuwa gidan Kwankwaso don su jaddada goyon bayansu ga shi Kwankwason.
Daurawa ya bayyana cewa da gangan Malaman Izala suka juya kalaman Kwankwaso don su harzuka magoyaba bayansu su tsani Kwankwaso.
Daurawa ya kara da cewa, Kwankwaso bai yi wani kuskure ba a kalamansa na cewa wasu malamai na fakewa da gemu su aikata sabo da goyon bayan cin hanci da rashawa da kama karya.
Ya ci gaba da cewa, da a ce Kwankwaso makiyin addinin musulunci ne da bai kaddamar da shari’ar musulunci a Kano ba, da kuma bai kafa Hisba ba, da kuma bai gina azuzuwa a makarantun Islamiyya ba da kuma bai aurar da zaurawa ba.

Wasu manyan malamai daga cikin wadanda suka yi wa Daurawa rakiya sun hada da: Sheikh Sani Ashir, Sheikh Malam Nazifi, Sheikh Abubakar Kandahar da Sheikh Gwani Sanusi.
Sauran sun hada da: Sheikh Alkali Mustapha, Sheikh Bazallah Kabara, Sheikh Buba Jada, Sheikh Isma’ila Mangu, Shiekh Malam Kabiru da dai sauransu.
Rahoto daga : Alummata.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: