Friday, 15 February 2019
Nasiha Da Jan Kunne Akan Yan kannywood Da Al:umma Nigeria Akan Zaben Gobe - Darakta Falalu Dorayi

Home Nasiha Da Jan Kunne Akan Yan kannywood Da Al:umma Nigeria Akan Zaben Gobe - Darakta Falalu Dorayi
Ku Tura A Social Media


Wajibine muji tsoron Allah mu masu yin zabe da wadanda zamu zaba. Domin yau ce ranar rabon KUDI ga masu TAKARA da ‘YAN KARBA
Lallai yana cikin ha’inci da cin amanar kai da ta al’umma, ka karbi kudi a gun Dan Takara domin biyan bukatar kanka kazo kuma kace Jama’a su zabe shi.

Duk mutumin da zamu zaba mu zabe shi domin amfaninsa da alkairinsa ga al’umma, ba domin bukatar kanmu ba. Mu zabi jagorori nagari wadanda suke aiki da dukiyarmu domin mu ba wadanda suke rabewa dasu da iyalansu da Yan korensu ba.

Tabbas abin da yake lalata kasa da al’ummar ta shine, dabi’ar nan ta me na samu, an san mutum bai cancanta ba amma sabida abin da zai bayar sai ai ta kokarin kururutashi ga al’umma su zabe, Lallai mu zabi cancanta domin alkairin al’umma baki daya.

Shugabanni wadanda za’a zaba, wajibinsu ne su ringa kallon gefan masu kushe su, cikin kushen zaka cin karo da abin da aka fada gaskiya ne sai kai amfani da ita domin gyaran mulkinka. Idan kuma karya ne ka sami kankarar zunubi, domin ba duka shugaba mutanen sa ke gayamar gaskiya ba.

Allah ka bamu Jagorori nagari.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: