Sunday, 3 February 2019
'N A S I H A T A G A R E K U: A yi siyasa me tsafta saboda akwai rayuwa bayan zabe - Abba Elmustapha

Home 'N A S I H A T A G A R E K U: A yi siyasa me tsafta saboda akwai rayuwa bayan zabe - Abba Elmustapha
Ku Tura A Social Media
Tauraron fina-finan Hausa, Abba El-Mustafa yayi wata fadakarwa akan siyasa inda ya jawo hankalin mutane da suyi siyasa mai tsafta cikin mutunci da girmama juna, saboda akwai rayuwa bayan zabe.
Ga abinda ya rubuta kamar haka:

'N A S I H A T A G A R E K U
Akwai rayuwa bayan zabe. Kar ka bari harkar siyasa ta hada ka rigima da wani. Kayi siyasa mai tsafta cikin mutunci da girmama juna. Ka girmama ra'ayin wanin ka shima ya girmama naka. Ta'addanci da bangar siyasa bata dace da duk mutum mai hankali ba, kar ka bari wani dan siyasa yayi amfani da kai wajen tayar da tarzoma a cikin al'umma. Kar kayi zaton 'yan siyasa suna amfani da kai ne don ci gaban kasar ka, suna amfani da kai ne su mulke ka don jin dadin rayuwar su. Ubangiji Allah yasa mudace.
Sai godiya'


Share this


Author: verified_user

0 Comments: