Wednesday, 13 February 2019
Mun Dade Muna Zagin Malamai (karanta)

Home Mun Dade Muna Zagin Malamai (karanta)
Ku Tura A Social Media

A lokacin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya bude Boda saboda Talakawa suna shan wahala ya zagu iya zaguwa.

A lokacin da Dakta Ahmad Ibrahim BUK yayi magana akan a sassautawa Talakawa haka shima a wannan dandali aka rika zaginsa.

A lokacin da Dakta Ahmad Gumi ya ce baya Buhari haka zagin safe daban da na rana.

Lokacin da Sheikh Bala Lau ya nemi ‘yan kungiyar Izala su zabi Buhari ya samu nasa kason zagin.

A dalilin bambancin akida ko fahimta mu kan takarkare mu zagi Malamin da ba tafiyar mu daya ba, wani lokacin har da kafirta juna.

A wannan dandali na ga wadanda suka rika zagin Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam da Albanin Zariya (Allah Ya Jikansu). Har hoton wani ya rungumi wata ake cire kan a sa na Ja’afar a la’ance shi.

Malam Lawan na Masallacin Triumph ba irin zagin da bai sha ba saboda yana Kawo gyara a mulkin Buhari. Takanas wani da ke ikirarin babban masoyin Buhari ne zai shiga gidan rediyon jihar ya keta masa rigar mutunci.

A lokacin da aka hana yin Gandun Shirya Fina-finan Hausa (Film Village) a jihar Kano Malamai sun zagu la’ada waje.

Malami a ko ina yake matukar yana kira abi Allah da ManzonSa abin girmamawa ne. Yana raye ko ya mutu. Ba irin barazanar da ba su gani a rayuwa ba, a zage su a ci zarafin su har kashe Malamai an yi.

Mutane da dama na cewa siyasa daban addini ma daban kuma bai kamata malamai da Sarakuna su shiga siyasa ba. Wannan ya sa muke ganin duk wani Malami da bai ce a zabi namu ba muna da ‘yancin mu zage shi mu ci zarafinsa. Amma abin tambaya shine akwai wani abu a rayuwar mu da Allah Ya kebance shi Ya ce kada a fadawa Musulmi gaskiya a kansa? Shin ita Siyasa ba Allah a cikinta? Idan ba Allah a ciki me ya sa Musulmi zai yi ta?

‘Yan siyasa na amfani da Malamai domin biyan bukatunsu, amma ba domin son Allah da kishin addini ba. Idan Bala’I ya zo su nemi Malamai a yi addu’a idan suna son cin zabe su nemi Malamai a yi addu’a.

Mu kuma magoya baya a bar mu da zagin Malamai don kare ‘yan siyasa. Amma Ni Maje El-Hajeej Hotoro  Malami mai tsoron Allah da yake kan tafarkin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya fi duk wani Dan siyasa daga Kansila zuwa Shugaban Kasa.

Malamai ba Allah ba ne ba kuma Mala’ikun Allah ba ne sannan ba Wahayi ake yi musu ba. Suna iya yin daidai suna iya yin kuskure, kamar yadda akwai masu fakewa da addini a cikinsu suna yaudarar Al’umma. Amma Malaman kwarai suna da daraja da mutunci da kima fiye da kowa saboda su Magadan Annabawa ne kuma zaginsu da cin zarafin su Halaka ne.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: