Friday, 8 February 2019
Mummunar Halayyar 'Yan Siyasa Mai Halakarwa - Dr Ahmad BUK

Home Mummunar Halayyar 'Yan Siyasa Mai Halakarwa - Dr Ahmad BUK
Ku Tura A Social Media


A Karatunsa na yau Juma'a da gidan Rediyon Dala FM na jihar Kano suka saka, Shehin Malami Dakta Ahmad Ibrahim BUK ya bayyana mummunar halayyar 'yan sisaya mai halakarwa.

Suna ji suna gani ana taba addinin Allah ba za su yi magana ba, suna ji suna gani a kwashe kudin jihar su. A lalata ilimi da tarbiyya, a jefa mutane a masifa a yi duk abinda za a yi ba ruwan su suna kallo.

Amma da zarar an taba shi ba zama lafiya sai ya tayar da jijiyoyin wuya, ya hana kowa sakatariya, saboda shi aka taba. Duk wancan barin mutane da talauci da jahilci da kuma kwashe dukiyar jiha da taba addinin Allah bai shafe shi ba. Kawai kansa da bukatarsa ya sani.

Daga nan sai ya tsallake ya koma wata Jam'iyyar ya ce wacce ya baro ba a adalci. A zaton su Allah ba Ya ganin su, kuma ba abinda zai yi musu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: