Sunday, 17 February 2019
Masifar Dake Kannywood Ta Wuce Misali - Adam A Zango

Home Masifar Dake Kannywood Ta Wuce Misali - Adam A Zango
Ku Tura A Social Media

"Ni ba 'dan daudu bane kuma ni ba 'dan maula bane. Sannan ni ba mushiriki bane, bani da malami ko matsafi. Da Allah ka'dai na dogara. Idan kuma akwai malamin da yace na taba zuwa wajansa ko kuma wanda ya taba bani kudi kyauta ba tare da nayi masa aikin komai ba to dan girman Allah kada ya rufa min asiri, tun daga kan 'yan siyasa, sarakuna, gwamnati, ko masu kudi ko 'yan mata. 

Duk abinda na mallaka arayuwa ta gumina ne ya bani ba dan adam ba. Motar hawa gida ko fili. Dan haka ba wanda ya isa yasa ni inyi abinda banyi niyya ba tunda ba wanda ya taya ni kare mutuncin kare daukaka ta ba."

"Don haka, hanya daya zaku iya dakatar da daukaka ta, hanyar itace ku dakatar da numfashina. Sai dai kuma kash hakan ba'a hannun ku yake ba. Ku ta yawo dani kuna bata min suna dan Allah ya fifita ni akan ku.

"Kunce min arne kunce min gay ('dan luwa'di) kunce min mai girman kai, amma duk da haka masoyana ba wanda ya guje ni basu daina sayan fina finai da wakokina ba.
"Haba dan Allah mai nayi muku duk wanda na taimaka a rayuwata sai ya dawo yana yakata". To na kai bango Billahillazi La'ilaha'illahu duk wanda ya kara taba ni sai na tona masa asiri."

"Sannan duk wanda ya rufa min asiri akan abubuwan dana lissafa Allah ya tona masa nasa. Ban kira sunan kowa ba a yanzu amma next time zan kira sunan kowaye idan ya kara bata min suna. Ina da 'yaya' ya zama dole na fara kare mutuncin kaina da martabata kafin ya yi affecting din su don Allah kadai yasan gawar fari. Sannan zan ja tunga ga makiyana na kannywood dan hakane kadai za'a banbance tsakanin aya da tsakuwa"

Masoyana ku gafarce ni akan abubuwan dana fada an kure ni ne.

Yadda a ko'ina ake samun nagari da bata gari hakazalika a cikin kannywood akwai nagari da bata gari, kuma wallahi billahi daga yau ba za'a kuma yi min kazafi nayi shiru ba dan kowa a cikinmu yasan kowa. Shi yasa idan akace mana jahilai bana damuwa domin nima nagano hakan. Tunda ance amfanin ilmi aiki da shi."

"Masifar da masana'antar kannywood take ciki ya wuce misali, saboda zalinci, fasikanci, riya, eye service (sa'ido) da kuma cin amana da ake aikatawa karara amma daga anyi magana sai ace matan cikin mu ke jawo mana. Wallahi matan mu basu da laifi domin addini bai taba ba mace damar zama ba mai kula da ita ba."

"Amma a kannywood fim mace daya ko yaro zasu yi sai kaga sun bude kamfanin kansu harma su dinga daukar sababbin 'yan wasa.
Babu tone tone domin da dama sun san kansu."

"Dan haka mu daina jin haushin maganar da wasu suke yi mana mu karba laifin mu gyara wata kila nan gaba kadan ayi alfahari da mu."

"Duk abinda na rubuta idan akwai karya wani ya fito ya karya ta ni ko kuma a kore ni."

"Duk wadda tace sai na neme ta kafin in sata a fim ta fito gidan television ko radio station ta fadawa duniya.Idan kuma ta rufa min asiri Allah ya to nata asirin." a cewar Adam A. Zango

Share this


Author: verified_user

0 Comments: