Saturday, 16 February 2019
Martanin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kan Kalaman kwankwaso : Hukuncin Kafirta Musulmi A Makarantar Ahlu sunnah

Home Martanin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kan Kalaman kwankwaso : Hukuncin Kafirta Musulmi A Makarantar Ahlu sunnah
Ku Tura A Social Media

DUK MUTUMIN DA YA SHEDA DA RUKUNAN MUSULUNCI BIYAR 
1  KALMAR SHAHADA
2  SALLAH 
3  ZAKKAH 
4  AZUMI 
5  HAJJI 
KUMA YA SHEDA DA RUKUNAN IMANI  SHIDA
1 IMANI DA ALLAH
2 MANZANNIN ALLAH 
3 MALAIKIN ALLAH 
4 LITTAFAN ALLAH 
5 RANAR LAHIRA 
6 KADDARA MAI DADI DA MARA DADI.

BAYA HALATTA A KAFIRTA MUSULMI  SABODA WANI,AIKI DA YAYI KO WATA MAGANA DA YA FADA WACCE AKE  GANIN TA SABOWA ADDINI SAI IDAN AN KAFA MASA HUJJA BAI JANYE BA. 
IBN TAIMIYYA YACE: KAFIRTA MUSULMI HAKKI NE NA ALLAH DA MANZON SA, BAYA HALATTA GA WANI YAYI WA WANI HUKUNCI DA KAFIRCI KO FASIKANCI KO BIDIA SAI DA HUJJA DAGA ALLAH DA MAZANSA,  BAYAN AN TSAYAR MASA DA HUJJA.
MANZON ALLAH SAW YACE:  DUK WANDA YA KALLI DAN UWANSA YACE MASA KAFIRI TO DAYA DAGA CIKI YA KAFIRTA. 
MANZON ALLAH SAW YACE : LAANTAR MUMUNI KAMAR KASHE SHI NE (A WAJAN LAIFI ) DUK WANDA YA JEFAWA WANI KAFIRCI KAMAR YA KASHE SHI. BUKHARI.6047
MALAM SHAUKANI YACE : KU SANI HAKIKA YIN HUKUNCI AKAN MUTUM MUSULMI CEWA YA FITA MUSULUNCI YA KOMA KAFIRI,  BAYA HALATTA GA DUKKAN WANDA YAYI IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA,  SAI IDAN YA KAWO HUJJA WACCE BABU GADA GADA A CIKINTA  A FILI TAKE KARARA KAMAR HASKEN RANA ASSAILUL JARRAR 4/ 578

IDAN KACEWA MUTUM KAFIRI KA YANKE MASA HUKUNCI KAMAR HAKA
KA FITAR DA SHI DAGA ADDINI
KA SAKI MATANSA
KA HALATTA JININSA
KA HANA AYI.MASA SALLAMA
KA HANA A KARBI SHEDARSA 
KA HANA AYI MASA WANDA DA SALLAH
KA HANA A BINNE SHI A MAKABARTAR MUSULMI 
KA HANA AYI MASA ADDUA 
KA HANA A RADA GADONSA 
KA HANA AYI MASA TABAKA 
KA HARAMTA MASA CERON ANNABI SAW
KA HARAMTA MASA SHIGA ALJANNAH 
KA DAWWAMAR DA SHI A CIKIN WUTA. 
DA SAURAN HUKUNCE HUKUNCAN RIDDA.

KAFIN MUTUM.YA ZAMA KAFIRI SAI AN TABBATAR CEWA 
BABU JAHILCI TARE DA SHI,
BABU WATA SHUBUHA DATA DAUKE SHI, 
BABU  WANI TAWILI GAMSASSHE. 
KUMA SAI AN ZAUNA DA SHI AN FAHIMTAR DA SHI ABINDA YA FADA DA  HATSARINSA,  YA FAHIMTA KUMA YAKI JANYEWA TO SAI A KAISHI KOTU, ALKALI YAYI MASA HUKUNCI DA RIDDA SANNAN YA BASHI KWANA UKU YA TUBA IDAN YAKI TUBA YAKI JANYEWA SAI AYI MASA HUKUNCI. 
WANNAN SHINE A TAKAICE ABINDA MALAMAI SUKA RUBUTA AKAN RIDDA.

BAYAN AN FARA YADA CEWA KWANKWASO YA SOKI SUNNAR GEMU DA DAGE TUFAFI,  MUN KIRA SHI A WAYA,  DANI DA WANI DOKTA DAGA JAMIAR BAYERO,  SAI SHI DOKTAN YA FARA MAGANA DA SHI,  YACE SHI BA SIFFAR ADDINI YAKE NUFI BA,  WASU MALAMAI MASU SHIGA IRIN WANNAN SHIGAR, AMMA SUNA AIKATA BA DAIDAIBA, SU YAKE NUFI, SAI SHI DOKTAN YACE TO IDAN HAKA NE SAI KA DINKA KAMA SUNAN SU DA AIKIN DA SUKA YI AMMA BA SIFFAR SU BA. DOMIN BASU KADAI BANE SUKE DA WANNAN SIFFA, 
KUMA MAGANAR MALAMAI DA SHIGA SIYASA SUNA DA YANCI DA DAMA HAR ZABE SU TSAYA KAMAR YADDA MUKE GANI , YANZU MATAIMAKIN SHUGABAN KASA FASTO NE, DAGA NAN SAI YA BANI MUKA KARA TATTAUNAWA, YAJI DADI YAYI GODIYA KUMA YACE ZAI GYARA, KUMA YA GYARA YA TURO MANA MUKAJI HAR YA KAMA SUNAN WASU MALAMAI NA SUNNAH YA YABA MUSU KOKARIN DA SUKE YI.

MANZON ALLAH YACE : DUKKAN MUSULMI AKAN MUSULMI HARUMUNNE DA JININSA DA DUKIYAR SA DA MUTUNCINSA. 
MUNA MATASA IDAN AN GAMMU SAI ACE GA MAKIYA ANNABI SAW.
GA MASU RASHIN LADABI GA  IYAYE .
GA MASU GEMUN DAN AKUYA. 
AMMA MAFI YAWA MASU FADAR HAKA TARE DA SU MUKE SUNNAH YANZU , SABODA HAKURIN DA MUKA YI DA ILMANTARWA HAR ALLAH YASA SUKA GANE,  MUCI GABA DA ILMANTAR DA WADANDA MASU SANI BA . ZA KUSHA MAMAKIN  HIDIMAR DA ZASU YIWA ADDINI WATARAN MAIMAIKON YAWAN SAKIN KAULASAN. 
MALAMAI SU SUKE HANGO ABU DA NISA.
ALLAH YASA MU GANE

Share this


Author: verified_user

0 Comments: