Saturday, 9 February 2019
Martanin Adam A Zango : Dalilina na Barin Buhari Na komawa Atiku

Home › › Martanin Adam A Zango : Dalilina na Barin Buhari Na komawa Atiku

Post By:

Ku Tura A Social MediaBayan kowa ya gani a ranar alhamis da ta gabata 07/01/2019 ne ya shedar da hakan na komawarsa bayan yaga comments da videos na yan uwan abokanan sana'arsa da Sunkayi masa na chanza sheka zuwa pdp.
Ga jawabin jarumin

" farko mutane su sani cewa na fadi duk masu bibiyata a social media cewa ni ba dan siyasa bane ni dan fim ne a karkashin kannywood.
Saboda haka na dade ina baiwa apc gudumuwa amma babu wani abin a yaba da ankayimin babu wanda ya taba Bani kudi a wannan tafiyar wanda sanin kowane nayi wakoki da bidiyo yi na bada gudumuwa ga tafiyar Shugaban kasa muhammadu buhari.

Shi buhari din bai sanin ba, el-rufai bai sanin ni ba, Ganduje ban sani ba basu san kowa ne ni ba.
Idan na fadi hakan nasan jama'a zasuyi mamaki duk irin yadda na bada gudumuwa tun 2015 zuwa yanzu abinda nake so ku lura da shin ka taba ganin hotun adamu zango da buhari ? Ka taba ganin Adamu zango da ganduje ? Shin ka taba ganin hotun adam Zango da el-rufai duk baka taba gani ba.
To babban dalilina na barin tafiyar muhammadu buhari shine irin wulakanci da ankayi min wanda shine naga bazan iya jure wannan wulakanci ba shiyasa na koma inda ake ganin girmana da mutuntani,sa'a nan ni buhari baiyimin komai ba.
Bugu da kari na kashe kusan biliyan biyu a fatiyar buhari wanda ba kowa yasan nayi hakan ba.
Wanda da komawata inda atiku ya tarban cikin nishadi da farin ciki.
Sai kuma magana ko gargadi ga apc akan yan kannywood da suke tare da ku kasan cewa wasu fa sunayinku ne dan kudi wasu kuma ba dan kudi ba ne".
Domin jin cikkaken bayyani sau kayi kalli wannan bidiyo.

Share this


Author: verified_user

1 comment:

  1. Kawai ka zuba jari ne a APC sai ka gano cewa ba patkn bacaka da arziki ba ne.karyar banza kai zaka iya kashe biliyon biyu na naira a zabe....mun gode wa Allah ma da muka gane ka.kuma ka yi daidai da komawa Pdp domin ka samu yan cenjin ka da kakashe a Apc saboda ko ma ka kashe a Apc ba za ka samu komai ba.kuma insha Allah buhari sai ya ci zabe, sai ka bar hasarar cenjin ka.

    ReplyDelete