Sunday, 10 February 2019
Malamin Makaranta Ya Yi Wa Dalibarsa ’Yar Shekara Shida Fyade A Maiduguri

Home Malamin Makaranta Ya Yi Wa Dalibarsa ’Yar Shekara Shida Fyade A Maiduguri
Ku Tura A Social Media
Babbar kotun ‘High Court’ a Maidugurin jihar Borno, ta tasa keyar wani malamin makaranta, dan kimanin shekara 19, Salisu Sani (an sakaya hakikanin sunan sa), hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10, bayan da ta same shi da laifin yiwa karamar yarinya, yar shekara 6 fyade.
Da yake amsa laifin sa ga kotun, wanda ke koyarwa a makarantar kudi a unguwar Ngomari, a birnin Maiduguri, bisa laifin aikata yin lalata da karamar yarinyar, kuma dalibar makarantar da yake koyatwa, inda ya yi amfani da ofishin malamai, a lokacin da aka tashi daga karatu- wanda ya yi amfani da damar wajen yiwa yarinyar fyade.
Tuni dai wanda ake zargin ya amsa laifin sa a gaban kuliy, kan cewa ya aikata laifin da ake zargin sa; na aikata laifin yiwa wannan karamar yarinyar fyade.

Wanda bisa ga yadda mai laifin ya yi ikirarin amsa laifin sa, sai mai gabatar da kara ya shidawa kotun cewa, wanda ya aikata laifin yiwa wannan yarinyar fyade, wanda kuma hakan laifi ne a dokokin da ke kunshe a sashe na 283 na dokokin jihar Borno, na 1994, wadanda suka fayyace matsayin wanda ya aikata irin wannan laifi.
Wanda a sa’ilin da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Wakil Gana, ya yanke wa mai laifin hukuncin zaman yari na tsawon shekaru 10, inda ya bayyana wannan lamari a matsayin abin takaice da Ala-wadai.
Mai shari’a Wakil ya bayyana matukar kaduwar sa dangane da yawaitar matsalolin fyade a jihar, musamman ga kananan yaran makaranta, wanda bisa ga hakan ne ya yi kira ga gwamnati tare da kungiyoyin da ba na gwamnati ba, a kan su sa ido sosai a irin wadannan makarantu

Share this


Author: verified_user

0 Comments: