Labarai

Malamai: In zasu tsine min sau 1000, sai Allah ya karamin daukaka – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, yayi karin haske akan maganarshi da yayi akan malamai da yace yakamata su dena amfani da mambarinsu domin zagi ko kushe su.

A ziyarar da wasu malamai suka kai masa a ranar Alhamis, Kwankwason yace kowa yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake, yace su malaman da yake magana akansu suma sunsan dasu yake.

Kwankwaso yace “Irin wadannan malamai ko zasu tsine min sau dubu sai Allah ya kara daukaka ni.

“Daya daga cikin abinda ya kawo wannnan muhawara shine rashin fadar sunaye ne, in anyi maganar masu shiga iri kaza, na ware da sauran banda ban fada ba. Kowa yasan a garin nan idan mukayi zagi a kasuwa munsan da wadanda muke.” a cewar Kwankwaso

A kwanakin nan dai Sanatan yayi maganar da ta ja hankalin mutanen jihar Kano dama kasa baki daya akan shigar malamai siyasa suna sukarsu. Lamarin da yaja malamai da yawa yi masa raddi na cewa ya taba sunnar Annabi (S.A.W)

Saidai wasu na ganin malaman suna sukar Kwankwason ne saboda bambantar ra’ayi, saboda wasu na cewa kar a zabi duka yan takarkarun da yake goyon baya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?