Labarai

Kotu Ta Amince EFCC Ta Kwace Kudin Patience Jonathan

Wata babbar kotun tarayya da ke Najeriya ta baiwa hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati damar kwace fiye da N1bn daga hannun Patience Jonathan.
Sanawar da EFCC ta fitar ranar Alhamis ta ce mai shari’a Lewis Allagoa na babbar kotun tarayyar da ke Kano ya baiwa hukumar izinin kwace N1,000,494,000 da kamfanin Magel Resort Limited, wanda ke da alaka da matar tsohon shugaban kasar Patience Jonathan ya boye a cikin banki.”
EFCC ta samu bayanan sirri cewa an boye makudan kudaden ne da ba a yi amfani da su ba a bankin Fidelity, in ji sanarwar.
Ta kara da cewa “bayan an samu wadannan bayanai ne hukumar ta soma gudanar da bincike inda daga bisani ta gano cewa mai dakin tsohon shugaban kasar da wasu ‘yan uwan Goodluck Ebele Jonathan ne daraktocin kamfanin. Sauran daraktocin su ne Oba Oba Tamunotonye, Goodluck Jonathan Aruera, Goodluck Jonathan Ariwabai da Esther Fynface.”
Daga nan ne kotun ta baiwa EFCC izinin wucin gadi na kwace kudin, a cewar hukumar. Kotun ta kuma bukaci a sanya kudin a Asusun Bai Daya na gwamnatin tarayya.
Patience Jonathan na cikin makusantan tsohon shugaban kasar, wadanda suka hada da tsofaffin ministoci da masu ba shi shawara da ake tuhuma da zarge-zargen cin hanci tun da Shugaba Buhari ya karbi mulkin kasar.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button