Sunday, 3 February 2019
Fim Din ‘Sadauki’ Ya Kafa Tarihin Farko A Babban Birnin Tarayyar Najeriya

Home Fim Din ‘Sadauki’ Ya Kafa Tarihin Farko A Babban Birnin Tarayyar Najeriya
Ku Tura A Social Media
Fitaccen fim din nan na Hausa da a ka dade a na sauraron fiowarsa, wato Sadauki, ya kafa tarihin zama fim din Kannywood na farko a ka fara nuna wa a manyan sinimun babban birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja.
A ranar Litinin din da ta gabata, 28 ga Janairu, 2019, ne Sadauki ya kafa wanna tarihi, inda a ka fara nuna shi a sinimun Silberbird Jabi da Wuse ko Central Area.

A lokacin da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta ziyarci sinimar Jabi ta shaida yadda wadanda su ka halarci kallon shirin su ka nuna gamsuwarsu da yadda fim din ya kayatar da su, inda bayan yawancin wadanda su ka fito bayan kammala kallon Sadauki su ke nuna alwashinsu na koma wa su sake kallon sa, saboda yadda ya yi matukar birge su.
Wata majiya ta shaida ma na cewa za a shafe makonni hudu a na a ka nuna fim din a sinimun. Fitaccen mai daukar hoto kuma darakta, wato Malam Hassan Giggs, shi ne ya shirya kuma ya bayar da umarni a cikin shirin na Sadauki, wanda Jarumi Adam Zango da Jaruma Fati Washa tare da Alasan Kwalle, Haruna Talle Maifata, Isah Ferozkhan, Tijjani Asase da sauransu su ka kasance jaruman shirin, wanda mashahurin marubuci Yakubu Kumo ya rubuta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: