Wednesday, 20 February 2019
Diyata ta fi kowa ilimi a gwamnatin Buhari kuma gudummuwar da ta bayar ko Buharin da mataimakinshi basu bayar ba - Buba Galadima

Home Diyata ta fi kowa ilimi a gwamnatin Buhari kuma gudummuwar da ta bayar ko Buharin da mataimakinshi basu bayar ba - Buba Galadima
Ku Tura A Social Media

A hirar da yayi da BBC, Buba Galadima, jigo a jam'iyyar PDP ya bayyana cewa, diyarshi Zainab ta fi kowa Ilimi a gwamnatin Buhari, yace irin gudummuwar da ta bayar koshi Buhari da mataimakinshi, Osinbajo basu bayar ba a tafiyar Gwamnatin.

Buba Galadima ya mayar da martani ne a yayin da aka tambaye shi cewa duk da cewa akawai 'ya'yanshi a cikin gwamnatin APC amma me yasa yake sukarta ?.

Ya ce diyarshi Zainab na da digiri na daya guda biyu da digiri na biyu guda uku da ACCA kuma da zata yi sauka a kasar Ingila Buharin da matarshi sun je bikin sannan shine ya bayar da ita aure kuma da ta haihu ta roki mijinta akan sawa dan sunan Buhari, to ai ya zama ubanta kenan, Injishi.

Buba Galadima ya kara da cewa amma duk da haka zai dauki mukami ya ba wani a gwamnatinshi amma ya hana Zainab?

Share this


Author: verified_user

0 Comments: