Thursday, 14 February 2019
Da Gaske ‘Yan Matan Yanzu Aure Suke So Ba Zaman Auren Ba?

Home Da Gaske ‘Yan Matan Yanzu Aure Suke So Ba Zaman Auren Ba?
Ku Tura A Social Media
A kullum auratayya ake yi, kuma a kullum auratayyan mutuwa suke yi ko mai ya sa?
Duk da yake wannan amsar tambayar bawani mai wahala ba ce ganin abubuwan da suke jawo macemacen auren suna da matukar yawa, sai dai wani abun da ya fi fitowa fili amma mutanen har yanzu basa ganinsa a matsayin daya daga cikin matsalolin dake haddasa mutuwan aure, shi ne yadda a yanzu mata burinsu kawai su yi aure amma ba sa tunanin yadda za su yi zaman aure domin ya samu dorewa na din-din-din. A yanzu mata basa kunyar fitowa filli su nuna wa duniya ta hanyar tallata kansu ta kafafen sadarwan zamani a kan suna neman mazan aure, abun sai ka dauka tamkar da gaske ne, amma kuma da zaran sun yi aure ka basu dan lokaci sai ka zaci kamar ba ita bace take tallata kanta da sunan neman mijin aure. Kama da ‘yan mata, zaurawa masu karancin shekaru harma wadanda suka haura shekaru 40 da haihuwa zantukansu basa wuce na Allah ya basu miji dai su yi aure su huta, amma wannan lamarin na rashin zaman auren bai ware kowa cikinsu ba.
Watakila masu karatu su ce ai su kansu mazan su ke janyo wa matan su kasa zaman aure ko da kuwa suna so, haka ne babu shakka, sai dai ba wannan bangaren na dauko ba, bangaren da na ke son yin magana a kai shi ne, bangaran da ya shafi ita macen wacce ita za a aura ba ita za ta aura ba, ita za ta zauna ba zauna mata za a yi ba, ita za ta sha wuya ko dadi babu mai sha mata su.
Mata a yanzu suna aure ne kawai domin a ce sun taba aure amma ba wai domin su zauna zama na har a bada ba a gidan auren.

Wasu matan hankalinsu kawai yana wajen aure ne kawai sobada sha’awa na jima’i ba tare da tunanin zaman auren ya wuce hakan ba. Da akwai wasu matan babban burinsu shi ne su yi aure su haihu daga nan kuma ko oho. Kamar yadda ake da wasu matan da suka dauki aure ya zamemasu garkuwa na cewa su matan aure banda wannan babu wani amfani da aure yake da shi a wajensu. Wasu kawai suna ganin shekarunsu sun ja kuma a ce basu da aure ba zai yiwu ba gara su, za su auri koma wa suka samu, ga kuma masu aure domin naga wacce ta yi. Uwa uba kuwa masu aure saboda tana mutuwar sonsa, sai an yi auren abun ya baiwa wadanda suka san su a lokacin buga soyayya mamaki.
Masu karatu aure ya wuce mutum ya gina shi da wadannan abubuwan dana ambata a sama, aure wani abu ne da ake shirya masa a san shi cikinsa da bayansa kamin a yanke shawarar yin sa. Banda rashin shiryawa, zaman aure yaushe ne mace za ta cewa namijin ya fito ya aure ta kawai saboda sun hadu ta Facebook ko wasu kafafen sada zumunta ba tare dama tasan dawa take mu’amala ba. A yanzu nan ba a gobe ba, akwai matan da suke shirin yin auren mazan da ba su taba haduwa ba, amma suna magana ta waya.
Kamar yadda ake samun wasu matan zuwan saurayi wajenta na farko, suke cewa namijin ya fi to. Wannan zakuwar da matan yanzu suke da shi na burin su dai aure, shi yake sa su su kasa zaman aure.
Matan sun fi maida hankali da bata lokacin wajen yadda za a shirya buki na kasaita wajen aurensu, maimakon maida hankali wajen gano wani irin namiji za ta aura. Mata sun fi tunanin su auri koma wani irin namiji ne, da dai a ce suna zaune a gida babu miji.
Tsabar lalacewa na matan yanzu, mazane ke bincike a kan irin matan da za su aura, ita kuwa ko oho. Ita dai a yi aure daga baya ta gano a wajen zama.

‘Yan uwa mata, da ki yi auren da za ki kasa zama ko za ki fiskanci bakinci da bacin rai a rayuwarki, gara ki zauna a gaban iyayenki kina musu hidima da biyayya maimakon gaggawan auren da baki shiryawa zaman saba. ‘Yar uwa ya kamata ki fahimci cewa idan zaman aurenki ya yi kyau, hankalinki zai kwanta, idan kuwa akasin hakan ne ya kasance to tabbas ke ka dai ce za ki fuskancin wannan ukubar. Shi dai aure ba a na yin sa bane saboda sunansa aure ba, aure ana yin sa ne domin a samu albarkan da ke cikinta hade da kwanciyan hankali da ke tattare da zaman aure.

Auren ko wani irin miji daya samu ba naki bane, akwai matakai na zaman da ake bi domin gano wasu alamu na mijin kirki da zai iya zaman aure da shi. ‘Yan uwa mata yana da kyau ku fahimci soyayya ta neman aure yana da bambamci da soyayya na zaman aure, kada kin yi tunanin irin kyautata miki ko soyayyan da yake nuna miki kamin aure, dole ne ya dore da hakan.
A shirin zaman aure mace idan har ta ce za ta auri namiji ne saboda tana matukar sonshi, nan ma za ta kasa zaman aure. Yana da kyau iyaye,’yan uwa harma da abokan arziki so rika taimaka wa mata na kusa da su, wajen shawarwarin yadda za su yi zaman aure kamin ma su fara tunanin yin aure, muddin bamu taimaka wa kawunanmu ba ta hanyar fadakar da ‘ya’yanmu da kannenmu illimin zaman aure ba, to kuwa mun dinga tara manya da kananan zawarawa a gari, duk al’umar da kuwa ta tara zawarawa kanana da suka san dadin namiji, tabbas wanna al’umar ba za ta gushe ba sai ta yi ta ganin abubuwa na assha. Kamar yadda yanzu muke ganin yawan shaye-shaye ga mata, karuwanci da kuma yadda jarirai a bola.

Da fatan Allah Ya kawo mana douki, ya kuma baiwa ma’aurata hakuri da juriyar zaman aure.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: