Sunday, 10 February 2019
Buhari ya ji tsoron daga hannun dan takara a Zamfara

Home › › Buhari ya ji tsoron daga hannun dan takara a Zamfara

Post By:

Ku Tura A Social Media


Rikicin 'yan takarar jam'iyyar APC a Zamfara ya hana shugaba Muhammadu Buhari daga hannun dan takarar gwamna a jihar.

A yayin yakin neman zabensa a Zamfara a ranar Lahadi, Buhari ya ce "duk gardamar da ake idan abu yana wurin shari'a za mu dakata."

Hakan dai ya kara tabbatar da cewa APC a Zamfara na cike da rudani bayan shugaban ya kasa daga hannun 'yan takara.

Hukumar zaben kasar INEC ta kara jaddada wa BBC matsayinta cewa APC ba ta da 'yan takara a zaben 2019 a Zamfara.

Kafin jawabin Buhari, gwamnan jihar mai barin gado Abdulaziz Yari Abubakar ya ce ba za su tilasta wa shugaban daga hannun 'yan takara ba kamar sauran jihohi.

"Ba za mu tilasta ma sa yin abin da yake da shakku ba."

"Idan mun tilasta ka cewa sai ka daga hannayen 'yan takara to muna ganin ba mu yi maka adalci ba saboda kasashen duniya za su kalubalanci matakin domin za a tilasta ka yin wani abin da kotu ba ta bada izinin a yi ba." In ji shi.

Gwamnan ya ce da yardar Allah da 'yan takarar APC za a yi zaben 2019.

Tun da farko, a wani gangamin siyasa gwamna Yari ya yi barazanar cewa zabe ba zai yiyu ba idan har babu 'yan takarar APC.

Ya ce bisa ga hukuncin da kotun Gusau ta zartar, INEC ba ta da hurumin hana wa 'yan takarar APC shiga zabe, inda ya ce kotun ta yi umurni ga INEC ta karbi 'yan takarar jam'iyyar.

A cikin jawabinsa a Zamfara, shugaba Buhari ya ce yana fatan kafin ranar Asabar, hukumar zabe za ta fito ta fadi dan takarar da ta yadda da shi.

Sai dai kuma Buhari ya yi kira ga mutane su fito su zabi wanda suke so, a gaban gwamnan Zamfara da ke gawagwarmayar tabbatar da kwamishinansa na kudi a matsayin gwamna.

Sauran 'yan takara sun kauracewa taron Buhari

Yakin neman zaben Buhari a Zamfara ya kara raba hankalin 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar.

Ana ganin zuwan Buhari bai yi wani armashi ba saboda rikicin na APC a Zamfara inda bangaren gwamnati ne kawai ya tarbi shugaban ba tare da sauran 'yan takara takwas da suka hada da mataimakin gwamna da ministan tsaro da kuma Sanata Marafa ba.

Tun da farko bangaren Sanata Marafa da ke rikici da bangaren gwamna Abdulaziz Yari ya yi kira ga shugaba Buhari ya soke zuwa yakin neman zabensa a Zamfara.

Sanatan ya ce ba za su iya cudanya da bangaren gwamnati ba domin tarbar Buhari da kuma wajen yakin neman zabensa ba.

Asalin rikicin APC a Zamfara

APC a Zamfara ta gaza gudanar da dukkanin zaben fitar da 'yan takararta na gwamna da na yan majalisar tarayya da na jiha.

Rikicin na APC a Zamfara ya samo asali ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha'awar takarar gwamnan a jam'iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.

Sau biyu ana shirya zaben fitar da gwanin a jihar, amma sai a soke shi saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam'iyyar a jihar.

Bangaren gwamnan jihar, yanzu ya fake ne da sakamakon wani hukuncin babbar kotun jihar a Gusau, inda alkalin kotun ya ce an yi zabe tare ba hukumar zaben kasar umurnin sunayen 'yan takararta a zabukan da za a yi batun da hukumar zabe ta yi watsi da shi.

Hukuncin wata babbar kotun tarayya a Abuja, ya tabbatar da matsayin hukumar zaben kasar na haramta wa duk 'yan takarar jam'iyyar APC daga Zamfara shiga zabukan kasar da za a yi cikin watan gobe da na jibi.

Hukuncin ya ci karo da na kotun jihar karkashin mai shari'ah Muhammad Bello Shinkafi.

Sai dai mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta kotun tarayya ta jaddada matsayin INEC inda ta ce jam'iyyun siyasa za su ci gaba da yin karan-tsaye ga ka'idojin zabe muddin suka kasa mutunta sharuddan da aka shata na jadawalin zabe.

Kotun ta ce hukuncin darasi ne ga sauran jami'yyun siyasa a nan gaba.

Rahoto :bbchausa.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: