Monday, 18 February 2019
Bikin Cikar Ali Nuhu Shekaru Ashirin A Fim Industri Tare Da Bikin Binne Fim Industiri Kashi Na Ɗaya - Fadila H Aliyu Kurfi

Home Bikin Cikar Ali Nuhu Shekaru Ashirin A Fim Industri Tare Da Bikin Binne Fim Industiri Kashi Na Ɗaya - Fadila H Aliyu Kurfi
Ku Tura A Social Media


Marubuciya Fadila H Aliyu Kurfi na taya Ali Nuhu murnar bikin cika shekaru Ashirin a Fim Industiri, sannan zan zaƙulu hanyoyi Ashirin da Jarumin ya bi domin rusa Fim Industiri ɗin gaba ɗaya.

Kwanakin baya na yi rubutu akan shirin Gundin Kannywood wanda Aminu Sharif Momo ke gabatarwa a tashar Arewa 24, inda na yi masa ƴar manuniya kan irin tambayoyin ƙure da ya ke yi ma abokan sana'arsa musamman mata wanda a ƙarshe idan baƙuwa ta gabatar da shirin ta tafi sai ka ji ana binta da sunaye kala-kala irinsu Jahila ba ta yi boko ba ko karatun addini wanda ni a ganina abin da ya ci doma tabbas ba zai bar awai ba, na yi masa gyara kayanka ne ba don cin fuska ko wani abu daban ba, tambayoyin ne da ba su da alaƙa da mu masu kallo saboda babu wata doka a fim industiri ɗin da ta tsara cewa ga adadin ilimin addini ko na boko da jaruman za su kasance da shi kafin shigarsu harkar ba, idan kuwa hakane babu dalilin ƴar ƙure-ƙure, na yi wancen rubutu ne saboda na fuskanci yana haƙa kuma yana binne kansa ne, idan an tashi za a kira ƴan fim jahilai har shi ke nan fa, wanda kowa yasan ba ayi masu adalci ba, akwai masu ilmi na boko da na arabi ke nan ya jama sana'arsa baƙin jini shi kuma a ciki yake ci. Alhamdulillahi shirin Kundin Kannywood na Arewa 24 za mu iya cewa an ɗan ƙara samun cigaba saɓanin da.

Wannan karon zan taɓo ruhin fim zuciyar Kannywood ɗin ne dukanta wato Sarki Ali Nuhu, ku fahimce ni zan yi masa gyara kayanka ne wanda ba zai taɓa zama sauke mu raba ba.
Duk da na san shi ɗan gaban goshi ne ba a faɗar kuskurensa, kuma wannan yana daga cikin babban dalilin da ya kai fim industiri ɗin ƙasa magashiyan. Sarki Ali Nuhu wanda ake kiransa da sunaye kala-kala irinsu Sarki, Sa, Yaya da sauransu domin daɗewarsa a Industirin ban da ja kan hakan daɗewa cikin bauta ai ƴanci ne, sannan ya samar ma matasa aikin yi da yawa kuma ya girme su a cikin harkar.

Sarki Ali Nuhu da za ka lura masarautar taka tana ta rushewa gine gine na ta zubewa, fadawa na cikin tsaka mai wuya, yayin da masarautar ta gama rogajewa gaba ɗaya saboda ta ɗauki harama, a ƙarshe za abar Sarki zaune saman karaga shi ɗaya tal yana mulki a masarautar Garin Babu Kowa.
Za ka zauna kai ɗaya da ƙaton rawani, zamanin da ka kai duba ga fadar ka ga babu kowa sai kai ɗaya to daga ranar ka zama ba Sarki ba, saboda mutum baya mulki garin da babu kowa kuma ko da yayi ba sunansa Sarki ba, idan ka tsallake daga Kannywood izuwa Nollywood da ke cen kudu an samu matsala, domin dai waccen sarautar taka ta Masarautar Kannywood kabar ta, cen kudu kuwa kasan akwai "manyan kuraye masu cin na gobe ƙiyama" ko labarinka ba ayi, kai za ka rinƙa bi kana "Sa" gara ka zauna ku gyara nan Arewa domin "duk wanda barno ta yi ma daɗi to fa bayan Madu yake.

1. Kuskure na farko  Sarki Ali Nuhu kai babban masoyin shirin finafinai Indiyawa ne wanda ba sai na faɗa maka ba, kasani al'adun Indiyawa ba su ko kama hanya da na Hausawa ba, Mai martaba Sarkin Kannywood ko a launin fata Hausawa mu baƙaƙe ne yayin da Hindu suke farare sol. To ya ya zaka cakuɗasu wuri guda kuma ka yi zaton haihuwar ɗa mai ido, kashi casa'in a cikin finafinan Hausa ba su da alaƙa da Hausawa da al'adunsu, to me zai burge Bahaushe da zai bata lokacinsa da kuɗinsa domin ya siya, Ali Nuhu kana yin fim cike da al'adun Indiyawa me zai hana ka ɗauki fim ɗin ka kai masu cen su siya idan suna da lokacin kallon wannan shirme, su fa wayewarsu ta wuce kallonku saboda tun da ga zubin labari ɗaukar hoto za su raina ku sannan al'adarsu na gaba da ta kowa a idanunsu, mu kuma da muke tare da ku kuna ganin kun fi karfin al'adarmu bayan kuma kuna cikin rigarmu ne ta Hausawa, da za ku yi adalci sai ku mayar da shi Ali Nuhu fim maimakon Hausa fim, ga al'adar Malam Bahaushe duk yanda mutum zai ɓata masa rai yakan tsaya ƙyam suna kallon juna suna magana ido cikin ido sai dai idan yana gaba da shi sai mutum ya sadda kansa ƙasa cikin ladabi, saɓanin cikin finafinanku da wai mutum yana magana saboda ɓacin rai sai ya juya ma abokin maganar sa baya, kamar dai Amita na magana da Mugembo a cen birnin Hindu, wannan al'adar Indiyawa ce ba ta Hausawa ba, duk yanda mutum ya kai ga sha'awar labari da yayi arba da irin wannan sai ya ji ransa ya ɓaci sannan abun ya yi masa kama da wasan yara ko shirme, gashi dai a fim Ali Nuhu kake kallo amma yana abu kamar wani Ba'indiye wanda ko a kala ba ku yi ɗaya ba, da yawa cikin jaruman masu koyi da Indiyawan maimakon su burge ka sai yaro ya rinka abu kamar ɗan daudu shi ala dole ga Sharukhan, ƙima da martabar fim ɗin Hausa tana zafgewa ta yanda sai wanda ba su waye ba kaɗai ke ɓata lokacinsu wurin kallo, ba "piracy" farasi ya kashe fim ɗin Hausawa ba Jarumai irinsu Ali Nuhu da Adamu suka kashe fim ɗin suna yin fim daidai da ra'ayinsu ba daidai da ra'ayin masu kallo ba shiyasa aka bar su da abin su, zan zo da hujjojina da misalai a rubutu na gaba.

Fadila H Aliyu Kurfi golden pen

Share this


Author: verified_user

0 Comments: