Sunday, 17 February 2019
Bidiyo : Duk wanda Baison Buhari Allah Ya Debemai Albarka - Sheikh Abubakar Giro

Home Bidiyo : Duk wanda Baison Buhari Allah Ya Debemai Albarka - Sheikh Abubakar Giro
Ku Tura A Social Media
Na kalli video na Sheikh Abubakar Giro Argungu yana tsinewa duk wanda bai son Buhari albarka, ga link nan a kasa domin saurarin wannan bidiyo ko downloading

Haka watannin baya muka saurari Dr. Ahmad Gumi yana yin tsinuwa ga duk wanda yayi sanadin zuwan gwamnatin shugaba Buhari

Shin akwai wata nassi da aka gano a cikin addinin musulunci inda akace duk wanda bai son Muhammadu Buhari shugaban tsarin mulkin yahudanci da nasara wato Demokaradiyyah a Nigeria ya cancani a tsine masa?, Malam Giro kayi babban kuskure

Kamar yadda muka fito muka nuna bacin rai lokacin da Dr. Ahmad Gumi ya la'ancemu saboda mun zabi Buhari to dole ma a yanzu mu fito mu nuna bacin rai saboda Malam Giro Argungu ya la'anci wadanda basa son Buhari, wannan ba daidai bane

Wannan kuskure ne, kuma daga dukkan alama wadannan commercial scholars da suke tsinewa al'umma suna yi ne don kare aljihunsu da kuma abinda suke samu a gurin 'yan siyasa, ba wai suna tsinuwar don Allah bane

Ga nan Femi Fani Kayode yana amfani da 'yancin siyasa yana ta cin zarafin addinin musulunci a Nigeria irin wadannan Malamai sun kasa mara raddi sun dawo suna tsinewa 'yan uwansu albarka saboda tsabagen son rai da neman abin duniya

Da irin wadannan Malamai babu shakka Musulunci yana tsaka mai wuya a Nigeria, babu yadda za'ayi ace yahudu da nasara da sauran makiya addinin Allah idan sun kawo mana hari ba zasuci nasara a kanmu ba saboda yadda wasu Malamai suka zama abin tsoro, lamarin sai dai addu'ah kawai

Allah Ya sauwake
Allah Ka jikan Malam Albaniy Zaria da Malam Ja'afar Kano.Domin saukar da wannan bidiyo kuyi ammafi da wannan link na kasaShare this


Author: verified_user

0 Comments: