Wednesday, 13 February 2019
Babu Mai Cin Mutuncin Addini Da Masu Addini Sai Ɗan Akuya - Sheikh Gadon Ƙaya

Home Babu Mai Cin Mutuncin Addini Da Masu Addini Sai Ɗan Akuya - Sheikh Gadon Ƙaya
Ku Tura A Social Media

A cigaba da mayar da martani da Malaman Sunnah ke yi dangane da kalaman tsohon Gwamnan jihar Kano Rabi'u Kwankwaso, bisa maganganun da yayi kwanakin baya inda ya soki lamirin malaman sakamakon tsoma baki a harkokin siyasa da suke yi, inda yace ba don Allah malaman suke batun siyasa ba suna yi ne domin neman kuɗi, ta hanyar yaudara ta aje gemu da ɗage wanduna.

Babban Malamin addinin Musulunci Sheikh Abdallah Gadon Ƙaya ya mayar wa tsohon Gwamnan da martani, inda ya bayyana cewar babu mai sukar masu addini sai Ɗan Akuya wanda bai da tarbiyya, sannan yayi addu'a Allah ya tozarta dukkanin mai izgli da sunnar Annabi.

Sheikh Gadon Ƙaya ya cigaba da cewar ko kaɗan ba za su saurarawa dukkanin wanda ke neman cin mutuncin sunnar Annabi ba, sannan ya buƙaci jama'a da su cigaba da addu'ar Allah karya laggon duk wanda ya mayar da cin mutuncin addini a matsayin ɗabi'ar shi, Allah ya wulaƙantashi tun a duniya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: