Thursday, 24 January 2019
'Yan Fim Masu Taimako A Kannywood Daga Darakta Aminu S Bono

Home 'Yan Fim Masu Taimako A Kannywood Daga Darakta Aminu S Bono
Ku Tura A Social Media

ALI NUHU

Wallahi ban san sau nawa ina tare da kai aka kawo maka labarin wane ya shiga matsala kuma ka taimakaba haka kawai kake neman mutum ka ba shi ko bai tambaye ka ba. Wannan al'ada taka sai take birge ni har nake fatan Allah Ya sa nima na taimaki wani dan masana'antar ba tare da ya tambaye ni ba.

IBRAHIM MANDAWARI

Dattijo kuma mai unguwar Mandawari Allah Ya ja da ran mai unguwa, shi mutum ne cikakke sai gashi yau a matakin mai unguwa yake cikin rufin asiri harma ace ana neman taimako kuma ya taimaka wannan shine ake cewa TANADIN GOBE A YAU

ADAM ZANGO

Na san shi sosai kamar yunwar cikina ban san sau nawa ya dauko tsoffin jarumai don yin aiki dasu ba musamman tarayyarsa da darakta Falalu Dorayi.  Sune suka canja marigayi IBRO zuwa jarumin da zai tsaya da kafarsa ya kuma sanya farashi daidai da shahararsa cikin mutunci da mutunta juna.

HADIZA GABON

Tunda nake ban taba ganin jaruma mai taimakonta ba, ba zan manta sanda kika je gidan DAUDU GALADANCI ba da irin alherin da kika je da shi ba. Duk da sanda yayi wasan kwaikwayonsa ba ma a haife ki ba ba zan manta taimakon da ki kaiwa abokanan aiki daban daban ba ciki har da ni.


RAHAMA SADAU


RAHAMA SADAU CE TA DAUKI NAUYIN KAI SANI GARBA SK ASIBITI DA DUKKAN ABINDA ZA AYI MAGANI
Assalam zanyi wani takaitaccen jawabi akanki @rahamasadau
Bama yiwa dan Adam adalci a sanda yayi kuskure muyita yayatawa Amma idan kayi alheri sai muyi gum da bakinmu
Nasani abinda zanyi bazaki so ba saboda kinyi kokarin boye alherin da kikayi don kwadayin ladanki agun Allah,dukda haka fadar mu bazata hana Allah yabaki lada akan kyakyawar niyarki ba mun sani kuna nan dayawa a kannywood kuna kokarin taimakawa badon a sani ba sai don zatin Allah.
ALLAH YA BIYAKI DA GIDAN ALJANNA

Share this


Author: verified_user

0 Comments: