Monday, 7 January 2019
Yadda Mace Za Ta Yi Zamantakewar Aure Cikin Sauki

Home Yadda Mace Za Ta Yi Zamantakewar Aure Cikin Sauki
Ku Tura A Social Media
Sau da yawa za ka tadda matsalolin gida ba daga uwar gida suke tasowa ba, wasu matsalolin tsakani da Allah mai gida yake kirkirar su, sai dai da wahala ka ga ya yi furuci da haka, gajiyawar namiji wajen rike gidansa takan bayyana ta fuskoki daban-daban, ko dai gajiyawa wajen kawo abubuwan masarufi wadanda suka shafi, tufafi, abinci da matsuguni, ko gazawa wajen tsawatawa, wani lokacin har da rashin sararin yin umurni da abu mai kyau.
Sau da yawa wasu mazan ba maza ba ne, sai su yi ta hargagi a waje, in suka shigo gida ka rasa kansu ka rasa kafarsu. Mu da matammu Allah (S.W.A) ya halicce mu daban-daban ne, ya yi mana kwakwalwa daban-daban, haka ma hanyoyin da muke tunani ko zartar da lamura, in dai namiji zai rika sauraron matsalolin gida ko zumunta daga wurin mace sannan ya yanke hukunci ba tare da dogon bincike da tunani mai zurfi ba, to ba shakka yana tattare da nadama, tun da har tunaninsa ya koma irin na mata.
A nan ba ina cewa ba su da tunani ba ne, amma hanyar da suke bi wajen warware matsalolinsu ba dai-dai suke da na maza ba, mace in abu ya dame ta ba ta bukatar daukar lokaci don zabin hanyar da ta dace wajen fuskantarsa. Tana iya tsai da ko mai lokaci guda ko ta bata shi, daga baya kuma sai a yi kuka gami da nadama, na sha jin mata suna ba da hakuri game da cewa “Ka san mu mata tunanimmu ba irin na ku ba ne, kenan daukar maganganunsu wajen yin saurin hukunci akwai matsala.

Wani abin kuma mace tana da saurin canjawa, dan abu kadan yana iya bakanta ma ta rai kamar yadda karamin abu yake iya faranta mata rai, kenan mai gida yana iya aiki da wannan dama wajen mallakar ta, a maimakon bata gidansa gaba daya, inda zai yi amfani da kalmomi masu dadi suna iya mantar da ita komai, su sanya ta farin ciki, in dai haka kawai ba za ka iya yaba kyawunta ba, to in ta yi kwalliya sai ka yaba, za ka iya samun damar fadin kirar da Allah ya yi ma ta, ko kyawun tufafinta ko adonta. Mata suna bukatar mazacansu su dunga yaban su, imam kwaliyansu kuma siffan da Allaha ya yi musu.
Kana iya fadin farin cikin rayuwar da kake yi da ita, da kasantuwarta uwar ‘ya’yanka, ko wace kake sa ran ta zama uwar ‘ya’yan na ka, kuma rayuwarka ba za ta kammala ba sai da ita, don tana yi maka kaza da kaza, in ma ba ka iya maganganun soyayya ba, duk lokacin da ka so wani abu a wurinta, sai ka san ya ya murya da yin batutuwa masu dadi. Ba wai wannan ne za su sa ta ba ka abin da kake so ba, sai dai za su saka ta ba ka su cikin dadin rai ba tare da jin kyashi ba.
Hatta maganganu irin na bacin rai akwai bukatar tattauna su kafin fitar da su. Bahaushe yana cewa magana zarar bunu, sannan ban da duka, duk mun yarda da cewa kai kakkarfa ne, in kana son ka nuna cewa kai namiji ne to nemi dan uwanka namiji, ba wai ka kare a kan mace ba, in ma kuskure ta yi kar ka yawaita aibantata ka yi ma ta nasiha, ka kare da gaya ma ta irin kaunar da kake ma ta, in ma da wata ‘yar kyauta nan kusa sai ka ba ta. To wanda yake zaton kausasawarka ya taras da tausasawarka ya kake zato?

Sannan ita ma tana bukatar ganinka cikin kyawawan kaya, kamar yadda kai ma kake bukatar ganinta haka, wani namijin ba ya bari wa matarsa zanin gado da ta sayi sabo zai keta ma ta da kafafuwansa, wato ba ya goge kirci, ba wai ga tsabta kadai ba. Namiji yana da bukatar tsayawa kyam wasu lokutan ta yadda zai iya kare kansa da gidansa, wani lokacin kuma yana da bukatar yin taushi don tarairayar iyalinsa. Wuce gona da iri ya kan kawo tashin hankali, sakaci kuma ya kan bata gida ne gaba da daya. To ya kamata mu dunga kulawa domin kawauce ruguza gidajanmu ba tare da mun sani ba.

Shawara Ga Matan Aure.

Ya kamata duk matar da ta tsinci kanta a dakin aure a wannan zamanin da muke ciki yanzu, ta gode ma Allah. Ba don komai ba, idan ta duba za ta ga wasu ‘yan mata irin ta, sun fi ta kyawun halitta da iya ado, amma har yanzu ba su samu mijin aure ba.
Don haka zai fi alkairi a gareki ki kudurce a cikin zuciyarki cewa gidan mijinki nan ne wajen neman aljannarki, idan kika bi mijinki sauda kafa to za ki yi samun aljanna cikin sauki, idan kuma kika sabawa mijinki to ki sani za ki hadu da fushin Allah.
Ki rike mijinki hannu bibbiyu, ki kula da tsaftar jikinki da tsaftar muhallinku.
Kuma ki zama ko yaushe a shirye kike domin biyan bukatar mijinki ko da bai nema ba.
Ki kiyaye mugwayen kawaye wanda ba za su rasa yi miki hassada ba. Tunda ke kin samu miji su kuwa ba su samu ba dole su yi miki hassada. Don haka sai ki kula da irin sawarwari da za su iya baki.

Ki kiyaye sirrin mijinki, kar ki gaya ma kowa, musamman ma kawayenki za su so su ji abin da yake faruwa don haka kar ki gaya musu.
Idan kuna da ‘ya’ya to ki kula da su, ki kula da tsaftarsu idan ma ‘ya’yan kishiyarki ne, to ki kula da su kamar yadda za ki kula da ‘ya’yanki.
Ki kiyaye dukkan amanonin mijinki musamman ma iyayensa da ‘yan uwansa da dukiyarsa domin duka Allah zai tambaye ki.
Matan aure ku sani Aaljannarku yana tafin kafar mazajanku, idan kun yi masu biyayya to za ku samu aljanna cikin sauki. Allah ka sa maza da mata mu yi aiki da wannan shawarwari domin mu gudu tare kuma mu tsira tare.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: