Wednesday, 9 January 2019
Ya Zama Dole Buhari Ya Sauka Muna Bukatar Shugaba Mai Cikakkiyar Lafiya Da Tausayin Al'umma Domin Shugabantar Kasar nan - Fati Kk

Home Ya Zama Dole Buhari Ya Sauka Muna Bukatar Shugaba Mai Cikakkiyar Lafiya Da Tausayin Al'umma Domin Shugabantar Kasar nan - Fati Kk
Ku Tura A Social Media
Jarumar masana'antar shirya Fina finan Hausa Kannywood, Fati KK ta bayyana shugaban kasa Muhammad Buhari ya hakura kawai ya dauka ba zai Iya mulkin kasar nan ba, domin kuwa Najeriya tana bukatar mutun ne jajirtacce mai cikakkiyar lafiya.

Lallai idan Al'ummar Najeriya suna so a dena kashe su, a dena korar su daga aiki, idan suna so su fita daga matsin tattalin arziki, su sami shugabanci na gari to lallai sai dai su Zabi Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi a zabukan 2019 dake tafe.

Buhari ya gaza bai zai iya kawo wani ci gaba a kasar nan ba, mulkin sa yana tafiyar hawainiya, lallai kawo gagarumin ci gaba a Kasarnan samar da aikin yi ingantaccen tsaro da ciyar da kasa gaba wannan sai Alhaji Atiku Abubakar.

Ina kira ga Al'ummar Najeriya da sauran masoya na dasu marawa Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi baya a zabukan 2019 dake tafe domin samun ingantacciyar rayuwa.


Facebook/jaridar dimokuradiyya

Share this


Author: verified_user

1 comment:

  1. Only a professional prostitute and Biased Northern girl would go against president Muhammadu Buhari.@FATI KK!

    ReplyDelete