Wednesday, 9 January 2019
Wakar ‘Mu Kurbi Ruwa Mu Zabi Buhari’ Ta Fi Duk Wakokin Da A Ka Yi Wa Buhari – Mudassir Kasim

Home Wakar ‘Mu Kurbi Ruwa Mu Zabi Buhari’ Ta Fi Duk Wakokin Da A Ka Yi Wa Buhari – Mudassir Kasim
Ku Tura A Social Media

A daidai lokacin da aka shiga kakar siyasa kusan za a iya cewa mawaqan Hausa kowa ya shiga waqe gwaninsa a cikin ‘yan takara na Jam’iyyu daban-daban, wasu sukan yi don aqidarsu ta son xan takarar, yayin da wasu kuma suke waqar ne domin su samu kuxi a wajen xan takara, ko da kuwa ba su da ra’ayin tafiyarsa. Su dai buqatar su ba ta wuce kuxin da za a ba su ba.
Fitaccen mawaqi MUDASSIR KASSIM yana xaya daga cikin mawaqa masu aqidar Buhari wanda ya daxe yana yin waqa domin tallata manufar Buhari tun kafin ya zama shugaban qasa. Bayan kuma ya zama shugaban qasa ya ci gaba da tallata manufofinsa.
A yanzu ma da kakar siyasa ta shigo ganin shugaba Buhari ya na neman zango na biyu, Mudassir Qasim ya canja salon waqar tare da yin wata sabuwar waqa mai taken A Kurvi Ruwa A Zavi Buhari , wadda yake son fito da ita a daidai lokacin da sabuwar shekara 2019 wato a farkon watan Janairun, don haka ne ma wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI ya nemi jin ta bakinsa a game da dalilinsa na yin wannan waqa da kuma abinda ya bambanta ta da sauran waqoqinsa. Don haka sai ku biyo mu don ku ji yadda tattaunawar ta kasance:
To Mudassir Kasim a xan jima ba a ji waqoqinka ba, amma a xan wannan lokacin mun samu labarin ka yi sabuwar waqa ta Shugaba Muhammadu Buhari. Za mu so ka yi wa masu karatu bayani a game da wannan sabuwar waqa taka.
To kamar yadda kowa ya sani shi dama mawaqi wani lokacin yakan koma ya shirya don ya fito da qarfinsa, kuma ba wai waqoqinsa ba ne ba a yi ana yi su kala-kala na faxakarwa da nishaxantarwa, da kuma wa’azi. To wannan karon ni saboda soyayyata ga shugaban qasa Muhammadu Buhari, idan ka cire ma maganar siyasa ni masoyin sa ne. ina qaunar sa tun lokacin da na tashi ina yaro, kuma ni ina qaunar qasa ta Nigeria kuma sai na ga cewa shi shugaba Nuhari yana qaunar qasar, wanda har zai iya ba da ransa da lokacinsa a matsayinsa na a yanzu yana shekara 76 ama yana qoqari ya ba da lokacinsa ga bautawa wannan qas,a don haka na ga cewa me ya kamata na yi domin na kare masa gwiwa, don ya ga cewar ‘yan qasar suna ganin qoqarinsa. Wannan ya sa na shirya wannan waqar na yi mata taken Mu Zavi Buhari kuma shi wannan amshi yana da ma’ana da abubuwa da masu nazari su za su fi yin nazari su fitar amma dai shi mawaqi ya san abin da yake nufi.
To amma dai duk da haka masu karatu za su so su san me ake nufi da A Kurvi Ruwa a zavi Buhari.
Eh, ka san shi mawaqi yakan yi magana ya murxe ta wadda kai mai sauraro na za ka fassara wa kanka, don haka ya rage naka ka yi fassara da kanka, amma dai an san ruwa abu ne da yake da daraja kuma abu ne da kowa yake so, don haka ne na ce A kurvi ruwa mu zavi Buhari. A wani vangare kuma na ce mu amshi kuxin mu zavi Buhari don da yawa ana ta raxe-raxin cewa ‘yan takararkari sun fito da kxui za su raba da qarfi su ci zave, ba tare da sun cancanta ba. Mu kuma muka ce idan an ba da kuxin ma a karva, kuma a zavi wanda ya cancanta ya dace da mulkin qasa.

A baya can ka yi waqa mai taken Ba Buhari ke yin arziqi ba, ko me ya bambanta wannan waqar da waccan?

Eh, bambancinsu shi ne waccan a lokacin da aka yi waqar ina wayar da kan mutane su gane cewa saurin da ake yi ba a ga canji ba a Gwamnatin Buhari su gane cewa ba Buhari ne yake yin arziqi ba, don ka rasa kuxi ba shi ba ne ya hana ka ba, sannan ba shi ke gyara zuciya ba, lalacewar da zuciyar kata yi a da kana tunanin sai wan ya zo ya gyara maka to ba fa shi zai zo ya gyara maka ba, kai ne z aa gyara da kanka don haka sai na ce kai mai gaggawar son ganin canji ka canja kanka, sannan za ka iya canja wani, to amma bambancinta da wannan shi ne yanzu mun ga canjin, mun ga irin hovvansa da ya yi don haka mu sake ba shi dama, tunda ya tsaya takara mu sake zavar sa ya qara zarcewa a gwamnati ta gaba, don muna sa ran zai yi abin da ya fi wanda yake yi a yanzu. To wannan shi ne dalilin daya sa na yi wannan waqa mu Kurci Ruwa mu zavi Buhari, kuma ina sa ran za ta fito a sati mai zuwa. A wannan shekara mai kamawa ta 2019.

Kamar yadda mawaqi yake saka kalmomi a baituka masu wahalar ganewa, kana ganin yadda ka yi amfani da su a cikin waqar za ta isar da saqon da kake so ka isar?

Ai yanzu da yake ita duiya a tafin hannu take, kuma da yawa yanzu mutane sun je makaranta, yanzu ba a jahalci don haka mutane sun waye a siyasa. Don haka ana gane waqoqin namu sosai yadda ya kamata, kuma wannan waqar da za mu fitar ta kallo ce, kuma ta sauraro, dama an san ta a gare kowa yana da ita, kuma waqa ce da duk waxanda ake yi a bidiyo da suka shafi wayar da kai da manufofin shugaba Buhari ba a tava yin waqa irinta ba, don ta qunshi ma’anoni sannan kuma shi wanda ya xauki nauyin buga waqar waqar Alhaji Dakta Abdullahi Bichi shi ne ya xauki nauyin buga ta da kuma yaxa ta, kuma ko da ka cire siyasa ma mu a masayin muna ‘yan Arewa hatta ‘yan kudu sun yarda da gaskiyar Buhari, to idan har wani ya sa ba za ka yarda da gaskiyarsa ba, don mu qoqarinsa da kishinsa ga wannan qasa shi ya sa muke taya shi saboda babu komai mu a gabanmu in ba qasar ba, idan har qasar ta samu kyakyawan makoma to mu kan da ‘ya’yan mu za mu samu kyakkyawar makoma.

Ka ce wannan waqar ta sha baban da waxanda aka yi wa Buhari ko me ya bambanta su?

To abin da ya bambanta su duk abin da muka faxa sai an nuna shi a aikace, kana kallon waqar kana ji kuma kana kallon ta a aikace, sannan mun xauki dogon lokaci muna bin ta don a samu hoto mai kyau kuma an yi mata kyakyawan tsari.

To kamar waccan waqar ta ka ta baya an ji tana a soshiyal media ko ita wannan za ka sake ta ne a kasuwa?

Na farko dai za a sake ta a soshiyal midiya, sannan za a raba ta ga qungiyoyi da suke tallafawa tafiyar shugaba Buhari za a buga ta a rabe ta a ko’ina, don haka ba ta sayarwa ba ce, don mu idan muka yi waqa irin wannan muna yin ta ne saboda kishin Buhari don haka duk masoyi ya cancana da ya same ta, mun yi mata tsarn da za ta yi sauqin samu a ko’ina mutum yake zai same ta a kafar yaxa zumunta.

To kuma masu satar fasaha fa? Kkun ba su dama su xauke kenan?

Eh, masu satar fasaha su yi ta bugawa fatan mu dai saqon ya je wajen kowa da kowa.

To wanne buri kakae so ka cimma da fitowar wannan waqa?

Ni burina shi ne duk wanda ya kalli wannan wa qar ya gamsu cewar abubuwan da muka faxa a kan waqar gaskiya ne, kuma idan zave ya zo na 2019 ya zabi Muhammadu Buhari.

Mene ne saqonka na qarshe?

To saqona na qarshe shi ne zave yana tahowa jama’ar qasa baki xaya a haxa kai a zavi cancanta kada mutum ya ba ku kuxi ku zave shi, sannan ina fatan a yi zave lafiya a gama lafiya.
To madalla mun gode.
Ni ma na gode.

Sources:hausaleadership.ng

Share this


Author: verified_user

0 Comments: