Tuesday, 15 January 2019
WA YA KASHE SANI SK? (Karanta)

Home WA YA KASHE SANI SK? (Karanta)
Ku Tura A Social Media


Da safiyar nan abokin aikina Sani Anwar ya kira ni wai da gaske Sani SK ya rasu?  Sanin ba shi da lafiya ya sa ni fadin Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un.

A ina ka gani?

Ga shi nan ana ta yadawa a Soshiyal Midiya?

 Tunda ka ga an sa da gaske ya rasun kenan.

"Ka dai bincika ka gani ko gaske ne" Ya Shawarce ni. Muna kammala waya na fara kira Sani SK.

"Jin ka ya fi ganin ka!"

Sunan da ya ke kira na da shi kenan. Wannan ya tabbatar min yana raye.

Aka ce wai ka rasu?

"Ina nan a raye ina ma asibitin Nassarawa"

A kwanakin baya haka aka yada makamancin wannan labarin akan Sani Moda wanda har yanzu yana raye.

Daga Maje Hajeej  Hotoro

Share this


Author: verified_user

0 Comments: