Tuesday, 15 January 2019
VIDEO :GANI YA KORI JI !!! Fitaccen tauraron fina-finan Kannywood Sani Garba SK. ya musanta labarin da ke cewa Allah ya yi masa rasuwa

Home VIDEO :GANI YA KORI JI !!! Fitaccen tauraron fina-finan Kannywood Sani Garba SK. ya musanta labarin da ke cewa Allah ya yi masa rasuwa
Ku Tura A Social Media


A ranar Litinin ne wasu mutane da ke amfani da shafukan sada zumunta suka yi ta baza labaran karya a kan cewa ya rasu bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.
Da ma dai tauraron na fama da rashin lafiya.
A hirarsa da BBC, sani S.K ya ce yana nan da ransa kuma yana samun sauki.
Ya bayyana cewa har ya gaji da amsa wayar tarho domin irin yawan mutanen da suke kiransa domin su ji ta bakinsa a kan ko da gaske ya mutu.
Amma dai tauraron ya ce yana fama da ciwon suga kuma ya gano hakan ne cikin 'yan kwanakin nan da ya je asibiti.
A baya dai an yada labaran karya a kan mutuwar wasu fitattun taurarin Kannywood, ciki har da Sadiya Gyale da Sani Modi.
Latsa wannan Link domin kallon video sa a bisa gabon asibiti yana jinya.Share this


Author: verified_user

0 Comments: