Tuesday, 1 January 2019
Sheik Kabiru Gombe, Buharin Malamai inji Sheik Awwal Maishago.

Home Sheik Kabiru Gombe, Buharin Malamai inji Sheik Awwal Maishago.
Ku Tura A Social Media


....Malam mai yawan masoya da yawan makiya.

Akwai wani Dr (ba zan fadi sunan shi da garin sa ba) har Youtube yake hawa ya duba adadin mutanen da suke kallon karatun Malam Kabiru Gombe da aka dora, Idan Sheik Kabiru Gombe na Larabci har natsuwa da bibiya yake yi domin ko zai gano kuskuren Malam.

Akwai wani Malami abokin Sheik Kabiru Gombe din ne tun shekarun baya amma yanzu yana cikin Maluma masu tsananin hassada da Malam Kabiru Gombe. Na taba ziyartar Malamin cikin abubuwa da yace a hirarMu wai- Yanzu daga Abuja zuwa Lagos ace Kabiru Gombe ba zai bi Mota ba sai dai jirgi?! Nace ai ko nima ba zan tafi Lagos daga Abuja ta mota ba sai idan ya zama dole.

Ire iren wadannan mutanen suna nan Dayawa, zaka sha mamaki idan kaji sunayenSu.
Saboda haka cikin Malamai ma akwai masu yi masa hassada duk da biyayya da yake musu, to ballantana cikin 'Yan bariki masu yakar shari'ar Allah!

Sheik Kabiru Gombe yana burgeni a mafi yawan lokuta saboda yadda yake baiwa Tauhidi nuhimmanci a karatukanSa da yadda yake tsoratarwa akan Shi'ah da warware shubuhohin su da tona musu asiri.

Allah ya kara kiyaye shi, ka kuma datar da shi da Daidai.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: