Friday, 4 January 2019
Real Madrid Ta Gargadi Manchester City Da Juventus Kan Casemiro

Home Real Madrid Ta Gargadi Manchester City Da Juventus Kan Casemiro
Ku Tura A Social Media
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana cewa dan wasanta, Casemiro, dan kasar Brazil bana siyarwa bane sakamakon rade-radin da ake na cewa kungiyoyin kwallon kafa na Paris Saint German da Manchester City da Juventus suna zawarcin dan wasan.
Casemiro, mai shekaru 26 a duniya yana daya daga cikin ‘yan wasan da mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Solari yakeso sosai kuma tuni yashiga cikin ‘yan wasa sha dayan farko na kungiyar a duk wasan da kungiyar zata buga.
Kungiyar kwallon kafa ta PSG dai tanason siyan dan wasan wanda take ganin shine zai iya maye mata gurbin Thiaggo Motta wanda shekarunsa suka kusa karewa a kungiyar kuma zai bar kungiyar bayan kakar wasa ta bana.
Yayin da ita ma Manchester City take son daukar dan wasan domin maye gurbin Fernandinho gashi kuma kungiyar ta rabu da Yaya Taure wanda yabar kungiyar a karshen kakar da take kokarin karewa.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, tuni PSG ta ware kudi, fam miliyan 50 domin taya dan wasan wanda kawo yanzu yana jiyya sakamakon raunin dayaji sai dai kociyan kungiyar ya bayyana cewa ya warke har yafara daukar horo.
Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Manchester City tana zawarcin dan wasan wanda take ganin zai kai fam miliyan 60 yayinda kungiyar kwallon kafa ta Juventus ma tafara tunanin neman dan wasan domin maye mata gurbin Khadera
Dan wasan yazura kwallaye 19 cikin wasanni 151 daya bugawa kungiyar kuma yana bugawa kasar sa ta Brazil wasa a yan kwanakin nan inda har gasar cin kofin duniya yaje a kasar Rasha wanda Farans atasamu nasara.
Sai dai kuma wani rahoton yana cewa dan wasan bashi da niyyar barin Real Madrid a daidai wannan lokaci da tauraruwarsa take haskawa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: