Kannywood

Northern_hibiscuss: ‘Abin da ya sa muka tara wa Ciroki kudi’ Sama Da N200,000

‘Mun taso muna kallon wasan Ciroki’

  • Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar
Shafin sada zumunta na Instagram na Northern_hibiscuss ya bayyana abin da ya sa suka tara wa Bashir Bala Ciroki kudi fiye da naira 200,000 a ranar Talata.
An fara tara wa daya daga cikin `yan wasan farko da suka shahara a masana’antar fina-finan Hausa ne bayan da aka samu labarin cewa yana tallan kunun aya.
Aisha Falke, mai shafin Northern_herbiscuss ta ce sun tallafa wa dan wasan ne saboda tausayi.
A wata hira da gidan talabijin na Arewa24 , Ciroki ya yi ikirarin cewa masu shirya fina-finai da jaruman Kannywood sun daina sanya shi a fim, shi ya sa a yanzu yake sayar da kunun aya.

‘Ban taba tunanin ina da masoya a duniya irin wannan ba’

Shafin Northern_hibiscuss ya wallafa gangamin nema wa dan wasan taimako.
Tsallake Instagram wallafa daga northern_hibiscuss

Karshen Instagram wallafa daga northern_hibiscuss
Sai dai kafin hakan, jarumin fina-finan Kannywood Ali Nuhu ya kalubalanci wani mai amfani da shafin Twitter cewa ya bayyana masa mutanen da abokin sana’arsa Ciroki, ya tallafa wa lokacin da tauraruwarsa ke haske a fagen wasan kwaikwayo.
Shi dai mutumin, wanda ke amfani da sunan Doctor Kiyawa, ya nuna rashin jin dadinsa ne kan yadda ya ce jaruman Kannywood sun yi watsi da Ciroki duk da cewa yana bukatar taimako.
Doctor Kiyawa ya yi zargin cewa mata kan shiga harkar fim cikin shekara guda su yi kudi amma mazan da suka kwashe shekara da shekaru suna harkar ba sa samun komai
“a Kannywood ne za ka ga mace ta shigo fim wannan shekarar amma ta fi wadda ya yi shekara 10 yana sana’ar fim kudi. Ali Nuhu, kai ne wadda yanzu jama’a suke gani da kima a Kannywood, don Allah ku yi wa [Chiroki] wani abu wanda shi ma ba zai manta cewa kun yi masa halacci ba.”.
Sai dai a jerin martanin da Ali Nuhu ya yi wa masu irin wannan korafi, ya kalubalance su da su nuna masa irin taimakon da Cirokin ya bai wa Kannywood.
“Zan yi maka tambaya: lokacin da Ciroki yake tashe wa ya taimaka wa? Maimakon haka, a kan kudi mene ne ba ya yi wa masu shirya fim? Ya kamata mu san abin da muke yi.”
Ya ce bai kamata a rika yi wa ‘yan Kannywood rashin adalci ba, wajen dora alhakin gazawar wani daga cikinsu a kansu.
Jarumin ya ce babu wani da ke Kannywood da zai taimaka wa Ciroki, yana mai cewa “ya kamata ya dawo masana’antar ya sasanta da masu shirya fina-finai, sannan ya ci gaba da aiki kawai.”
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button