Labarai

Nine zan kafa cikakkiyar Gwamnatin dimokradiyya : Atiku ya harbo sabbin makaman siyasa masu linzami daga Legas

Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyya PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kushe gwamnati mai ci yanzu da kuma bayyana gwamnatin damokaradiyyar da zai kafa mutukar aka zabe shi a zabe mai zuwa.

Wazirin Adamawan ya lissafo dokoki masu amfani da zai tabbatar matukar aka zabe shi kamar haka
 :-

1. Zamu samar da aiyukan yi ga mutanen kasar nan kamar yadda kowa ya sani cewa babu aikin yi wanda hakan ne yasa talauci yayi yawa.

2. Hadin kai tare da tsaro a kasar nan: rashin hadin kai shine tushen rashin zaman lafiya. A saboda hadin kai ne ake samun fadace fadacen addini da kabilanci.

3. Yaki da fatara da samar da abinci.

4. Gina kasar da take duban muhallin doka da fifita ta akan kowanne mutum: kundin tsarin mulki kasa kadai shine zai zamo tushen dokar kasa.

6. Zamuyi aiki da bangarori masu zaman kansu na kasar nan don gano hanyoyin rage yawan cin bashi, matsalar karbar ninkin haraji da kuma samar da hanyoyin cinikayya tsakanin mu da kasashen kettle.

7. Zamu yanta guraren tattalin arziki tare da siyarda duk wata ma’aikata da ta gaza.

8. Zamu habaka kananan sana’o’i don su samarwa mutane abin yi.

9. Zamu habaka fannin ilimi da kiwon lafiya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?