Thursday, 3 January 2019
Nasarar Da Film Din Yaki A Soyayya Ya Samu Ta Kannywood Ce Gaba daya

Home Nasarar Da Film Din Yaki A Soyayya Ya Samu Ta Kannywood Ce Gaba daya
Ku Tura A Social Media


Tun lokacin da aka saki film din YakiASo

yayya a sinimar Film house da ke Kano, rahotanni ke ta bulla kan yadda film din ke samun karbuwa a wurin 'yan kallo.

A zahiri, musamman idan aka yi la'akari da yadda masana'antar ke tafiya, Yaki A Soyayya ya samu gagarumar nasara. Saboda haka na yi nazari kan manyan ababen da zan iya cewa suna maqasudin nasarar film din.

LABARI:
Labarin film din ya dace daidai da matsalolin masoya a wannan zamanin, wanda a wasu lokutan suke rasa ainihin me yake faruwa da junansu.

Yadda aka tsara labarin film ya yi ma'ana matuka, duk iya bin kwakkwafin mutum, ba zai iya gano me zai faru a gaba ba, sabanin wasu finafinan da kana fara kallo, ka san kwanan zancen.

DANDALI (LOCATION)
Watau masu shirya finafinan Hausa har yanzu sun kasa gano cewar yawan amfani da location iri daya wajen shirya finafinai na rage kwarjini. Za ka film goma, amma kusan gidajen da aka yi dauke su duk daya ne. Shi kuma dan kallo kullum yana son ganin abu sabo musamman a yanayin da zai kayatar da shi.

An yi kokari matuka wajen samar da sabbin wurare yayin daukar shirin Yaki A Soyayya.

JARUMAI:
Babu abinda za a cewa jaruman film din nan sai jinjina. Sun nuna wa duniya tabbas qanana jarumai idan suka samu horaswa za su iya yin abun kirki. Akwai mamaki matuka, kan yadda film din da babu wani babban jarumi ko darakta ya shafe tarihin kowane film a sinima.

DARAKTA:
Alfazazee Muhamnad yana bada umarni a finafinai, amma bai taba samun damar da ya barje gumin basirarsa ba sai a Yaki A Soyayya. Yadda ya sarrafa jaruman wajen samar da sakon da ake da bukata ya cancanci yabo da jinjina.

TALLA (PROMOTION)
Wasu finafinan ana kashe kudi kuma a bata lokaci wurin yin su, amma wajen tallatawa sam, sai ka rasa ina lissafin furodusa ya yake. Dole film yana buqatar tallata wa a-kai a-kai, wannan shi zai bawa 'yan kallo damar bibiyar yaushe zai fita, har ila yau, a rika jin ra'ayoyin 'yan kallo bayan sun kalla. Hakan zai sa wadanda ba su zo ba garzayowa don su ganewa idonsu.

LOKACI:
Watau na dade ban ga film din da aka dauki tsawon lokaci ana shirya shi kamar YakiASoyayya ba. Duk da cewa jaruman da suka ja ragana

Share this


Author: verified_user

0 Comments: