Uncategorized

Nafi Shekara Biyu Zuwa Uku Ina Wannan Nazarin da Bibiyar Comments a Social Media – Dr Jabir Sani Mai hula Sokoto

‘Yan kudancin Nigeria, Musulmin su da kiristocin su, ‘yan APC da ‘yan PDP, basu zagi da cin mutuncin Professor Yemi Osinbajo Koda ko sun saba masa a ra’ayi.
Kiristocin Nigeria tare da banbancin darikun su basa zagi da cin mutuncin Mathew Hassan Kuka, duk da cewa, da yawan su basa biyar sa sallah. Wannan shi ake cewa “Disipline”( not technical meaning).
Abin mamaki, anan Arewa musamman ta Musulmi, abu ne mai sauki Yaro dan kasa da shekara 30 ya zagi Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alh. Atiku Abubakar,  Dr. Ahmad Gummi, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ko wani daga cikin manyan Malamai ko Sarakuna,  ko yayi masa cin zarafi don dai ya sabawa ra’ayin sa.
Babban abin lura anan shine, mutum biyu baza suyi sabani ba cewa, daga 1999 zuwa yanzu ‘yan kudu sun fimu cin gajiyar demokradiyya nesa ba kusa ba. Ashe ba zagi da cin mutuncin manya kesa a samu ba!!
Bayan Manzon Allah S. A. W. ba wanda biyar maganar sa ko ra’ayin sa yake cilas. Ra’ayin kowa ijtihadi ne, yakan yiyu ya zama daidai yakan yiyu ya zama kuskure. Amma rashin yarda da ra’ayin wani baya nufin sai kayi masa cin mutunci da cin zarafi.
Ina kira ga Musulmin Arewa musamman matasa da muji tsoron Allah, mu kama bakunan mu da hannayen mu daga cin mutuncin mutane musamman Wadanda Allah ya baiwa manyan shekaru da matsayi a cikin mu, dasunan sabanin ra’ayi. Wannan bai taba zama wayewa da ci gaba a kowane civilasation ba, haka kuma bazai taba zama addini ba.
Allah Ya dora mu a hanya madaidaiciya. Ameen

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button