Labarai

Muna Allah-wadai da dirar mikiyar sojoji – Daily Trust

Daya daga cikin fitattun jaridun Najeriya, Daily Trust ta yi Allah-wadai da wani dirar mikiya da ta ce sojojin kasar sun yi wa ofisoshinta uku, inda suka kama wasu ma’aikatanta tare da kassara ayyukanta na ranar Litinin.
Tun da farko, wasu sojoji cikin fararen kaya ne suka je ofishin jaridar a binin Maiduguri da misalin karfe 4:30 ranar Lahadi, suka gudanar da bincike kafin su yi awon gaba da ‘yan jarida biyu Uthman Abubakar da kuma Ibrahim Sawab a cewar wata sanarwar da Babban Editan Jaridar Dailytrust, Mannir Dan-Ali ya fitar kuma aka buga a shafinta na intanet.
Sanarwar ta yi zargin cewar matakin ba ya rasa nasaba da labarin da ta buga kan yadda rundunar sojin kasar ke kokarin kwato wasu garuruwa da rahotanni suka ce ‘yan Boko Haram sun kwace a baya-bayan nan.
Ta ce kamfanin Media Trust ya yi Allah wadai da matakin, kuma ya bukaci su sako ma’aikatansa biyu da suka kama a Maiduguri.
Haka zalika, jaridar ta kuma bukaci a mayar mata da kwamfutocin da sojojin suka tafi da su daga dakin labaranta.

Ta ce kafin janyewar sojojin sai da suka binciki dakin labaran jaridar inda suka yi awon gaba da kwamfutoci da dama da kuma wani ma’aikacinta a ofishin Abuja, wanda suka sako shi daga bisani bayan ya shafe tsawon lokaci tsare a barikin Mogadishu.
Hakan a cewar Daily Trust ya kawo cikas ga ayyukanta na wallafa kwafe-kwafen jaridar da za ta fitar ranar Litinin din nan.
Baya ga dirar mikiyar a ofisoshinta na Maduguri da Abuja, sanarwar ta kuma ce wasu sojoji cikin mota bakwai sun yi wa ofishinta na Legas tsinke da misalin karfe 9:00 na daren Lahadi.
Ta ce a lokacin da sojojin suka je ofisoshinta na Maiduguri da kuma Abuja, sun rika tambayar ko ina wadanda suka rubuta babban labarinta na ranar Lahadi?
Ita dai, rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta tare da ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro sun je ofisoshin jaridar ne don gayyatar ma’aikatanta da suka buga wani labari a ranar Lahadi.

Sanarwar da daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar ta ce buga labarin ya saba da doka kuma barazana ne ga tsaron kasar.
A cewarta matakin ya ci karo da sashe na daya da na biyu na dokar kiyaye sirrin hukuma.
Sannan kuma zai bai wa ‘yan ta-da-kayar-baya damar sanin lokacin da sojoji za su kai musu hari, abin da kuma hatsari ne ga dakarun da ke yaki da Boko Haram, in ji ta.
Har ila yau, sanarwar ta ce an gayyaci wadanda ke da hannu ne da kyakkyawar manufa, da nufin sanar da su game da illar hakan ga tsaron kasa.
A cewarta, rundunar sojin Najeriya ba ta da niyyar cin mutunci ko hana ‘yan jarida aikinsu kamar yadda dokar kasa ta tanada, amma ba za ta lamunci duk wata kafar labarai da za ta rika aikata wani abu na nuna goya baya ga yan ta’adda ba ko kuma kokarin kawo cikas ga hukumomin tsaro a kasar ba.
Sannan kuma tabbatar da cewar gayyatar na dan bincike, sanna kumazasu gurfanar da duk wadna suka kama da laifi a gaban kot.

Rahoto: bbchausa.com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button