Sunday, 6 January 2019
Mbappe ne Zai Maye Gurbin Messi A Duniya

Home Mbappe ne Zai Maye Gurbin Messi A Duniya
Ku Tura A Social Media
Sa’ilin da Messi da Mbappe suka rungume juna bayan karawa tsakanin Faransa da Argentina a gasar cin kofin duniya a Rasha, sai ya zamanto kamar wata alama ce ta komawar kwarewar Messi kan Mbappe.
Daukacin wadanda suka kalli wasan da aka yi tsakanin Faransa da Argentina na cin kofin duniya a Rasha, sun bar filin wasan tare da yakinin cewa sun kalli wani wasa na musamman, wanda za a dade ana tunawa sannan kuma daya daga cikin ‘yan wasan da suka buga wasa a filin da ya burge kowa
Shekarun Kylian Mbappe 19 ne kacal, amma ya samu nasarar zura kwallo biyu a wannan karawa, ya kuma yi wasa mai kayatarwa inda har ya samo wa kasarsa bugun fanareti wanda shi ne ya haifar da kwallo ta farko da aka zura a ragar Argentina, a karawar wadda aka tashi Faransa na da kwallo 4, Argentina na da 3.

Mbappe bai zo duniya ba a lokacin da kasarsa Faransa ta lashe kofin duniya, sa’ilin da ta karbi bakuncin gasar a shekarar 1998 saboda an haifi dan wasan ne a ranar 20 ga watan Disamba na shekarar 1998, kuma yanzu haka yana wasa ne a kungiyar Paris St-Germain da ke Faransa.
Fam miliyan 166 PSG ta biya akan dan wasan hakan yasa ya zama dan wasa na biyu mafi tsada a duniya, kasa da yadda PSG din ta sayi dan wasan Brazil Neymar, daga Barcelona a kan kudi Fan miliyan 200
Mbappe na da hazaka sosai ciki har da tunani cikin hanzari, yana amfani da dukkanin kafafunsa yadda ya kamata, ya iya cin kwallo da ka, yana da kwazo, sannan ya iya hangen inda zai zura kwallo a cikin raga.
Bayan karawar tsakanin Faransa da Argentina a kofin duniya a shekarar data gabata, ga abin da tsohon dan wasan Ingila Alan Shearer ya ce game da Mbappe: “A shekara 19, a ce ya yi wasa mai kayatarwa irin wannan a gaban Lionel Messi, yayin da miliyoyin al’umma ke kallo, wannan ba karamar hazaka ba ce.”
Mbappe dai Shi ne matashin dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci kwallo biyu a wasa guda daya a gasar kofin duniya tun bayan Gwarzon dan wasan Brazil Pele, da ya ci biyu a wasan karshe tsakanin Brazil da Sweden a shekarar 1958.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: