Wednesday, 2 January 2019
Matakan Mallakar Miji (Mata zallah)

Home Matakan Mallakar Miji (Mata zallah)
Ku Tura A Social Media
Wani mutum ne, Allah ya hore masa ikon karin aure, ya auro
yarinya me hankali da dabara, tarbiyya gata da nutsuwa gami da
Addini. Da Amarya tazo gida sai ta karewa rayuwar gidan Kallo, sai ta fahimci Uwargida tana da sakaci akan Abubuwa kamar haka:-

1- kullum sai mijin su ya kusa makara kafin ya fita saboda jinkiri wajen girkin safe (break fast).
Dan haka in girkin ta yazo sai tayi kwazo wajen sallamar me gida da wuri. Da uwargida ta fahimci haka itama sai ta kara himma ta daina sakaci.

2- Uwargida bata iya kaiwa mijin ta ruwan wanka ba, Amarya ta
fara kaiwa, itama uwargida ta soma.

3- Sai Amarya ta dauki wata Tsurfa duk sanda megida ya cire
kayansa a dakinta yana fita sai ta fito tsakar gida ta wanke su
tasss, ta shanya ta goge, da Oga ya shigo sai yayi tashi mata Albarka. Itama uwargida ta fara.

4- Sai Amarya ta kara fito da wani Sabon Salo (inji bahaushe yace wai kiran Sallah da Usur) kawai sai ta sa aka siyo mata brush na goge takalmi da Man goge takalmi
different colors, kawai ta fara goge takalman megida! Ita Uwargida ta sa aka siyo
mata ranar girkinta sai ta goge takalman megida.

5- Kawai sai amarya ta shigo da
wata sabuwa (wai inji 'yan Cha-Cha). Da safe sai Amarya tasa Hijab ta Dakko Ruwa Abokiti da Omo da Duster, ta nufi Gate, ta hau motar Oga da durza (wanki), Kawai sai
Uwargida tafito aguje ta saka Kuka. Ta hau Amarya da Duka tana cewa:-

Shegiya wallahi bazaki kwacemin miji ba. In banda iskanci ina mace ina wankin mota in ba makirci kika shirya ba. Allah ya isa tsakanina dake!!!

Hhhhh Ni aganina in duka gidan aure zai zama kishi yana tafiya ne a haka to tabbas da sai muce maraba da kishiya. Allah ta'ala yana cewa:-

ﻭﻓﻲ ﺫﺍﻟﻚ ﻓﻠﻴﺘﻨﺎﻓﺲ
ﺍﻟﻤﺘﻨﺎﻓﺴﻮﻥ !!!!

Mallam

Share this


Author: verified_user

0 Comments: