Labarai

Mata ta maka mijin ta a Kotu saboda tura ‘ya’yan su Almajirci a Kaduna

 0Wata mata mai suna Jamila Abubakar ta maka tsohin mijin ta Isah Aliyu a kotu dake magajin Gari, Kaduna saboda tura ‘ya’yan su makarantar Allo da yin bara da yayi a wani kauye kusa da su.
Isah dai ya saki Jamila ne kimanin watanni uku kenan. Sannan kuma bayan haka sai ya tattara ‘ya’yan su ya tura su makarantar Allo a wani kauye.
Jamila ta roki Kotu da ta tilasta wa tsohon mijin nata ya dawo da wadannan yara cikin gari inda suke makarantar Boko da Islamiyya da ita kuma ne dama ta saka su a makarantan.
A nashi jawabin a gaban Alkali, Isah ya karyata wannan zargi da matar sa ta yi ya ce dalilin da ya sa ya saki matar sa shine don taki bin sa kauyen da yake zama.
A karshe Alkali ya yanke hukuncin tabbatar da saki a tsakanin su sannan ya umarci Isah ya taho kotu da wadannan yara nan da mako guda.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?