Friday, 4 January 2019
Mata Ayi Hakuri Dan Allah (wannan Karatun Mata zallah ne)

Home Mata Ayi Hakuri Dan Allah (wannan Karatun Mata zallah ne)
Ku Tura A Social Media

✓ Idan aurenki yayi jinkiri ko kika rasa miji da*
*wuri:* tuna sayyida khadija (r.a), da tayi hakuri sai
Allah ya azurta ta da mafi alkairin mazaje a
gidan duniya kuma Annabin Allah (s.w.t.)..
✓ Idan Allah bai nufeki da yin aure ba gabaki*
*daya:* tuna da nana maryam (a.s) da yadda Allah ya mata albarka a gidan duniya da lahira, kuma
ya yabeta da kamewa a cikin littafinsa mai
tsarki, dukda cewa batayi aure ba...
✓ Idan Allah (s.w.t) bai azurtaki da haihuwa ba:*
kiyi hakuri kada ki daga hankalinki ko ki damu da
zancen mata: ki tuna matar Annabi Zakariyya
(a.s) da tayi hakuri sai Allah ya dubi zuciyarta ya
azurta ta da haihuwa dukda da cewa ta tsufa
shekarunta sun tafi...
✓ Idan Allah ya jarrabeki da azzalumin* *miji mai sabawa Allah da bijerewa hanyarsa:* sai ki tuna
Asiya matar fir'auna, da Allah ya dubi zuciyarta
sai ya sanyata ta zamto daka cikin
shuwagabannin matan Aljannah..
✓ Idan Allah ya kaddara miki rabuwa da mijinki ko ya sake ki: sai ki tuna fadin Allah (s.w.t).
"Idan suka rabu to Allah zai azurta kowa da
rabonsa.."
✓  Idan Allah yayiwa mai gidanki rasuwa kada kiyita sanya damuwa a zuciyarki har ki rinka furucin cewa bazaki taba samun wani wanda ya*
*fishi alkairi ba:* ki tuna ummu salma matar Abu-
salma, (r.a), da mijinta yayi wafati sai Allah ya
canja mata da wanda ya fishi shine Annabi
Muhammad (s.a.w.), sabida kasancewarta daka cikin masu cewa:Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, a lokacin musiba...
Ki sanya a zuciyarki cewa arzikin Allah yana
zuwa..
Kada ki kwallafa ranki ko kisa ido ga arzikin da
Allah yayiwa wata ta kusa dake ko yar'uwarki..
Ki sani cewa Allah yana sane da halin da kike
ciki, domin shi ya halicceki, kuma ya fiki sanin kanki da damuwarki...
Kada ki damu da abunda mutane ke furtawa a
kanki, domin basuda abinda suka isa su miki idan ba wannan zancen ba, kuma shi baya cutarwa...
Allah ya shiryar da bisa tafarkin Shari'a....
*Pls u can share the message to circulate*

Share this


Author: verified_user

0 Comments: