Thursday, 3 January 2019
Manchester United Za Ta Siyi Dan Wasan Baya Na Roma

Home Manchester United Za Ta Siyi Dan Wasan Baya Na Roma
Ku Tura A Social Media
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana zawarcin dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Roma, Kostas Monalos, wanda yashafe shekaru biyar a kungiyar kamar yadda rahotanni suka bayyana. Manchester United ta dade tana zawarcin dan wasan baya sakamakon yawan zura mata kwallo a raga da akeyi inda ta nemi dan wasan baya na kungiyar Tottenham, Toby Alderwereild da kuma Harry Maguirre na Leceister City. Bayan da kungiyar takasa siyan dan wasan baya a farkon wannan kakar a karkashin tsohon kociyan kungiyar, Jose Mourinho, yanzu Manchester United ta juya akalarta wajen neman dan wasan baya na Roma wanda akayi wa kudi fam miliyan 32. Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa dan wasan ya kasa cimma yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Roma wanda hakan yasa kungiyar tafara tunanin siyar da dan wasan kuma Manchester United tana daya daga cikin kungiyoyin da suke zawarcinsa. 

Manolas dai yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan baya da ake ji dasu a gasar siriya A ta kasar Italiya kuma a kwanakin baya ma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta nemi dan wasan bayan. Dan wasan mai shekara 27 a duniya ya bugawa kungiyar Roma wasanni da dama sannan kuma dan wasa ne mai zura kwallaye a raga duk da cewa dan wasan baya ne.Share this


Author: verified_user

0 Comments: