Tuesday, 22 January 2019
Majalisar kasa ta amince da dubu 27 mafi karancin albashi

Home Majalisar kasa ta amince da dubu 27 mafi karancin albashi
Ku Tura A Social Media
Majalisar kasa a Najeriya ta tsayar da naira dubu 27 a matsayin karamin albashin ma'aikata a jihohi da kamfanoni da masana'antu masu zaman kansu.
Majalisar ta kuma tsayar da naira dubu 30 a matsayin karamin albashi ga ma'aikatan tarayya.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron majalisar a fadarsa a ranar Talata wadda ta kunshi tsoffin shugabanni da tsoffin alkalan alkalan Najeriya da kuma gwamnoni da shugabannin majalisa.
Kungiyar kwadago ta NLC da ta dade tana jayayya da gwamnati kan karin albashin, ta ce tana nazari game da wannan ci gaban nan gaba za ta bayyana matsayar da ta yanke, kamar yadda shugabanta Kwamred Ayuba Waba ya shaida wa BBC.
Ministan kwadago Chris Ngige ya ce a ranar Laraba za a mika kudirin ga majalisa domin ta amince.
Ya ce majalisar kasa ta amince da naira dubu 27 bayan nazari kan matsayar da kwamitin duba bukatar karin albashin ya yanke ta naira dubu 30 da dubu 24 da gwamnatin tarayya ta ce za ta iya biya da kuma naira dubu 22,700 da gwamnoni suka ce za su iya biya.
An dade ana kiki-kaka kan albashi mafi karanci da gwamnatoci da kamfanoni za su biya ma'aikata Najeriya.

Jadawalin albashi

Har yanzu akwai jihohin gwamnoni suka gaza biyan naira dubu 18 mafi karancin albashin da ake biyan ma'aikata a kasar.
Gwamnonin jihohin sun ce yana da wahala su iya biyan dubu 30 a matsayin karamin albashi sai idan a sake diba tsarin kudaden da suke samu daga Tarayya,

Share this


Author: verified_user

0 Comments: